You are on page 1of 133

FATAWOYIN DA SUKA SHAFI

MATA MUSULMAI GUDA (150)

NA

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA


AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA

FITOWA TA DAYA
JULY, 2018

1
‫بسم الله الرحمن الرحيم‬
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da
amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad manzon tsira
da mutanen gidansa da sahabbansa.
Hakika ilimin fiqhun musulunci yana daga cikin ilimomi masu
muhimmanci wadanda mutane suke bukatarsu saboda
lamuransu na yau da kullum, wannan yasa malamai suka
himmatu wajen dawwana wannan ilimin da kuma karantar
das hi.
A cikin wannan takardu mun tattaro muhimman FATAWOYI
wadanda suka shafi ‘yan’uwa mata daga cikin amsoshin
tambayoyinmu da muka rubuta a kafafen sada zumunta
(social Media), muna rokon Allah ya sanya albarka a cikinsu
ya zamar da su ambato mai kyau gare mu bayan
rayuwarmu.

2
1. SHIN MAI CIKI TANA IYA YIN HAILA ?

Tambaya:
Malam mai ciki za ta iya ganin Haila ?
Amsa:
Yawanci idan mace ta dau ciki jini yakan daina zuwa mata,
Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da
yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya
kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da
shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan
kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa
da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba
biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen
haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda
hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba? Anan
malamai sun yi sabani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila
ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali
duk jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai
ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba,
kuma babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi
ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i,
kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun
Ahmad.
Don haka yana tabbata ga mai ciki mai haila abin da yake
tabbata ga mai haila mara ciki sai a gurare guda biyu :

3
1. SAKI- Ya haramta a saki matar da idda ta wajaba a gare ta
idan tana haila, amma mai ciki ya halatta a sake ta a cikin
haila, saboda sakin matar da bata da ciki ya sabawa fadin
Allah ( Kuma ku sake su a farkon iddarsu) Suratud Dalak aya
ta 1, wato a farkon tsarkin da bai take ta a cikinsa ba. amma
sakin mace mai ciki tana haila sakin ta ne ga iddarta,
wannan ya hada da tana cikin haila ko tana cikin tsarki,
saboda iddarta tana kasancewa ne da haife wannan ciki, don
haka bai haramta a sake ta ba, bayan an yi jima’i da ita.
2. Mace mai ciki idan ta yi haila ba za ta yi idda da ita ba,
saboda iddar ta tana kasancewa ne da haife cikinta, wannan
ya hada da tana haila ko bata yi, saboda fadin Allah
madaukaki ( Iddar mata masu ciki tana kasancewa ne idan
su ka haife cikinsu). Suratud Dalak aya ta 4 Don neman karin
bayani duba : Dima'uddabi'iyya shafi na 11.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
4/2/2012

2. HUKUNCIN SAKIN MAI HAILA


Tambaya:
Malam mun samu rikici da matata ko ya halatta na sake tana
haila?
Amsa:
Ya haramta a saki mace lokacin da take haila, saboda fadin
Allah "Ya kai Annabi idan za ku saki mata, to ku sake su a
farkon iddarsu) Suratu Addalak aya ta farko, wato a farkon
tsarkin da ba ku take su a cikinsa ba. Ana nufin a halin da za
su fuskanci idda sananniya, wannan kuwa ba ya faruwa sai

4
idan ya sake ta tana da ciki ko tana cikin tsarkin da bai take
ta ba, domin idan ya sake ta a cikin haila to ba ta fuskanci
idda ba, saboda hailar da ya sake ta a ciki ba za’a kirga da
ita ba, haka kuma idan ya sake ta tana da tsarki bayan ya
sadu da ita, domin bai sani ba shin ta dauki ciki ta yadda
iddarta za ta zama irin ta mai ciki ko kuma ba ta dauka ba ta
yadda za ta yi idda da haila, saboda rashin tabbacin haka sai
sakin ya haramta. Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim cewa
: Ibn umar ya saki matarsa tana haila, sai Umar ya bawa
Annabi s.a.w. labari, sai Annabi s.a.w. ya yi fushi, sai ya ce
"ka umarce shi ya mayar da ita sannan ya rike ta har ta yi
tsarki sannan ta yi haila, sannan ta yi tsarki, sannan in ya so
ya rike ta ko kuma ya sake ta kafin ya sadu da ita, wannan
ita ce iddar da Allah ya umarta a saki mata a ita" ana togace
gurare guda hudu wadanda sakin mace mai haila yake
hallata :
A. idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya
sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila, saboda
anan bata da idda, sakinta ba zai zama ya sabawa fadin
Allah madaukaki (Ku sake su a farkon iddarsu) ba.
B. idan ta yi hailar ne tana da ciki
C. idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, (KUL'I) to anan
babu laifi ya sake ta tana haila
D. Idan ya yiwa matarsa I'laa'i kuma aka yi watanni hudu bai
dawo ba.
Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/2/2013

5
3. MANUFOFIN DA SUKA SA AKA HARAMTA ZINA!
Tambaya:
Assalamu alaikum malam Ina son karin bayani game da
manufofin sharia akan haramta zina.
Amsa:
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya zo don ya kare
tsatson Dan'adam da mutuncinsa, don haka ya shar'anta
aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin
da haramta zina ya kunsa :
1. Katange mutane daga keta alfarmar shari'a.
2. Samar da Dan'adam ta hanya mai kyau, ta yadda za'a
samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi
ta hanyar zina, to ba za'a samu wanda zai kula da shi ba
yadda ya kamata.
3. Saboda kada nasabar mutane ta cakudu da juna.
4. Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina
tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja.
5. Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a
bayyane.
6. Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe
matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya
kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa,
sai fitintinu, su yawaita.
7. Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane.
8. Kare mutuncin yaron da za'a Haifa, domin duk yaron da

6
aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci. Allah ne
mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/4/2013

4. SHIN YA HALATTA NA AURI WANDA BA

AHALUS-SUNNA BA ?
Tambaya:
Salam Malam ya halalta mace ta auri wanda ba dan Ahlul
sunnah ba? Don Allah ina son aba mu hujjoji saboda ta samu
abinda zata kare kan ta da shi.
Amsa:
To 'yar'uwa Annabi s.a.w. yana cewa : "Idan wanda kuka
yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura
masa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba
ta : 1084, Malamai suna cewa wannan hadisin yana nuni
akan cewa duk wanda ba'a yarda da addininsa ba, ba za'a
aurar masa ba, wannan sai ya nuna cewa duk wanda
bidi'arsa take kaiwa zuwa kafirci, bai halatta a aura masa 'ya
ba, don haka duk dan shi'an da yake zagin sahabbai ko yake
kafirta su bai halatta a aura masa 'ya ba, saboda ba musulmi
ba ne, domin ya karyata Allan da ya yarda da su, haka sufin
da yake allantar da shehunansa, ko yake ganin sun fi
annabawa, kuma yana sane yake hakan, ba jahili ba ne ko
kuma wanda yake da shubuhar da za'a iya warware masa .
Amma duk mai aikata bidi`ar da ba za ta kai zuwa ga kafirci
ba, to ya hallata a aura masa 'ya, kamar wanda yake yin
maulidi saboda son Annabi s.a,w.
7
Allah ne mafi sani ,
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
1-12-2014

5. HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE SABODA


KYANTA??
Tambaya:
Malam: Akwai wani hadisi da yake Magana kan cewa kowa
ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jindadin
kyan, ko dan kudinta Allah zai hana masa jin dadin kudin,.
shin hadisin akwai shi kuma ya inganta?
Amsa:
Ga yadda hadisin ya ke : DUK WANDA YA AURI MACE
SABODA KUDINTA, ALLAH ZAI KARA MASA TALAUCI, DUK
WANDA YA AURI MACE SABODA KYAWUNTA ALLAH ZAI KARA
MASA MUNI Saidai a cikin hadisin akwai Abdussalam bn
Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka
hadisin bai inganta ba, kuma ba za'a kafa hujja da shi ba.
Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/1/2014

6. YA YAGA TAKARDAR SAKIN KAFIN MATARSA TA GANI


Tambaya: Assalamu alaikum, malam shin idan mutum ya
rubuta takardar saki ya aje, sai wani ya gani shin matar ta
shi tasaku?
Amsa:
Wa alaikum assalam To malam matukar ya rubuta da niyya
kuma yana cikin hayyacinsa ba takura masa aka yi ba, to ta
saku, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi : "Allah ya yafewa al'umata abin da ta riya a
8
zuciyarta, mutukar bata fada ba, ko ta aikata" ka ga kuma
rubutu aiki ne.Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya kasance yana zartar da abubuwa da yawa ta
hanyar rubutu, ka ga ya zama hujja kenan. Wannan shi ne
mazahar Abu-hanifa da Malik kuma shi ne zancen Shafi'i mafi
inganci. Duba Al-mugni : 7\486 Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28/1/2014
7. SUFRA DA KUDRA DA HUKUNCINSU

Tambaya:
Dan Allah Malam Ina bukatar bayani akan "KUDRA da kuma
SUFRAH", Allah ya saka da Alkhairi.
Amsa:
To 'yar'uwa, wannan yana daga cikin mas'aloli masu
mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwaka game da
hakan:
Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwan
ciwo, ya fito daga gabanta.
Kudra kuwa na nufin : ruwa ya ringa fitowa daga farjin
mace, wanda kalarsa ta ke kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da
baki wato kamar ruwa gurbatacce,
Dangane da hukuncinsu kuwa : idan daya daga cikinsu ya
kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila
kafin ta sami tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan
kuma bayan tsarki ne to ba haila ba ne saboda fadin Ummu
adiyya mun kasance ba ma kirga sufra da kudra bayan tsarki
a cikin haila) Abudawud ya rawaito shi da sanadi mai
inganci,

9
A hadisin A’isha kuma (Mata suna aiko mata da abin da suke
sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan
da yake kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi
gaggawa har sai kun ga farin ruwa ya fito, ta yadda za mu yi
amfani da hadisin Ummu adiyya bayan an sami tsarki,
ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila
ba, hadisin A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana
cikin haila ta yadda za ta kirga da su. Don neman karin
bayani duba: Dima'uddabi'iy a shafi na: 8
Allah ne mafi sani
6.12.2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
8. ADADIN SHAHIDAI DA INGANCIN SHAHADAR
WACCE TA MUTU A NAKUDAR CIKIN SHEGE?
Tambaya:
Assalamu alaikum Allah ya gafarta Mallam don Allah ina
Matsayar Malamai akan wadannan Mas'aloli, tare da
ambaton dalilai daga Qur,ani/Hadithi: Mutane nawa ne Ya
tabbata a Alqur,ani/Hadithi Sunyi Mutuwar Shahada? Domin
wani Dalibi abokina ya ce: Albani ya Ambaci : 9 a cikin
AHKAMIL JANA'IZ na duba ban gani ba, sannan idan Mace ta
mutu ayayin haihuwar Cikin Shege, shin itama ta yi
Shahada?
Amsa :
To dan'uwa shahidai suna da yawa: sun haura guda tara :
Ibnu- hajar yana cewa : "Mun tattara hadisan da suka yi
bayani akan shahidai sai muka samu sama da nau'i ashirin
na shahidai, Fathul-bary 6/43 hakanan Suyudi a littafinsa mai
10
suna : Abwabissa'adah fi asbabissa'adah, ya kawo sama da
guda talatin
Ka ga daga ciki, akwai wanda ya mutu a fagen daga, da
wanda ya mutu da ciwon ciki, sai wanda ya mutu a lokacin
kwalara sai kuma wanda ya mutu ta hanyar rusowar gini, sai
wanda ya nutse a ruwa, Hakanan wanda ya mutu wajan kare
dukiyarsa, da wanda kunama ko miciji ya harba, sai ya yi
ajalinsa, haka matar da ta mutu wajan haihuwa, dama
wanda namun daji suka cinye shi Haka wanda aka kashe shi
saboda kare iyalansa, duk wadannan sun tabbata a cikin
hadisai. Saidai wasu malaman suna ganin akwai sharuda
kafin mutum ya samu shahada:
Daga ciki kada ya zama: Ba ta hanyar gangaci ya mutu ba,
kamar mutumin da bai iya ruwa ba, ya shiga kogi, sai ya
mutu, sannan kar ya zama ta hanyar sabo ya isa zuwa
shahadar, kamar matar da ta mutu wajan nakudar cikin
shege, ko bawan da ya gujewa mai gidansa, sai ya mutu a
hanya.
wasu malaman suna ganinin hakan ba sharadi ba ne, tun da
hadisan ba su kayyade ba. Don neman Karin bayani duba:
Fataawal-kubra na Ibnu-taimiyya 3/22 da Mugni A l-muhtaj
3/166
Allah ne mafi sani
9-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

9. ANA YIWA IYALINA WANKAN JEGO, KO YA HALATTA?

Tambaya:

11
Salam malam don Allah ka taimaka min ka amsa tambaya
ta. ni dai malam gaskiya hankali na ya ki kwantawa
sakamakon al'adar wankan jego da ake yi a kasar hausa.
iyalina ta haihu an kawo wata tana yi mata wanka, to malam
ya hukuncin ya ke duba ga haramcin nuna tsaraici ga wani,
don Allah malam ka daure ka Amsa don hankalina ba'a
kwance yake ba.
Amsa:
To malam akwai hanyoyin na zamani wadanda za'a iya
amfani da su ba tare da an yi wankan jego ba, kamar amfani
da kwayoyi na asibiti, saidai idan ya zama babu makawa sai
an yi wankan na jego kuma wata ce za ta yi mata, kamar ya
zama haihuwar fari ce kuma babu halin da za'a iya sayen
kwayoyi saboda talauci, to hukuncin wannan zai yi daidai da
hukuncin likitan da take kula da lalurar mata, saboda shi ma
wankan jego ana yinsa ne saboda magani. A shari'ance ya
wajaba ga likita ya yi taka-tsantsan wajan kallon al'aurar
mara lafiya ta yadda ba zai kalli wani bangare na al'aurar
mara lafiya ba sai gwargwadon lalura, domin daga cikin
ka'idojin shari'a shi ne duk abin da ya halatta saboda lalura,
to ya wajaba a tsaya gwargwadon lalurar, wannan ya sa idan
da zai kalli sama da haka, sai ya zama mai laifi a wajan Allah.
Al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace tana farawa ne daga
cibiya zuwa guiwa a zance mafi inganci, don haka mai
wankan jego za ta kalli gwargwadon abin da ya wajaba ta
kalla don tabbatar da lafiyar mai jego, idan kuma akwai

12
hanyar da za ta bi ta yi mata wankan ba tare da kallon
al'aurar ta ba, to wannan shi ne ya wajaba.
Duba kwatankwacin wannan mas'alar a Alkawa'idul kulliya na
Usman Shabirr shafi na : 222
Allah ne mafi sani
14-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

10. TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA


Tambaya :
Assalamu alaikum, Mal Na kasance ina tsotsan azzakarin
mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin
mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa :
To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saidai
ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin
mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin
haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da
wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar
cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda
neman kariya Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara
aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan
sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da
su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.
Domin karin bayani duba: Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul
Khalil 3/406.
Allah ne mafi sani.
21-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

13
11. ABUBUWAN DA AKE SO MIJI YA FI MATARSA DA SU

Tambaya: Assalamu alaikum, malam da fatan kana lafiya,


wasu tambayoyi nake rokon Malam daya taimakamin da
amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu, shin malam wai
akwai wasu abubuwa uku da ake so mace tafi mijin da za ta
aura da su,sannan shima akwai abu guda uku da akeso ya
fita da su?, sannan akwai wadanda sukayi musharaka
akansu, da fatan malam ya sansu, kuma za'a taimakamin da
su, nagode.
Amsa :
To dan'unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa,
ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku : ta fi shi a kyau, ta
fi shi kananan shekaru, ta fi son shi, sama da yadda yake
sonta . Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta
kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta Ana so su hadu a abubuwa
uku : ya zama akwai yaran da yake hada su, ya zama
addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan
aka samu wadannan uku-ukun, to za'a samu jin dadin aure.
don neman karin bayani ka nemi shirin minbarin malamai
da na yi a freedom radio Kano na ranar : 3 ga Ramadhan
1434 A.H
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

12. SHIN ZAN IYA YIN DILLANCIN HOTUNAN 'YAN


MATA?
TAMBAYA:

14
Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada
hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure?
AMSA:
Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba
muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli
mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin
hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa: "Idan dayanku yana
neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi
zuwa aurenta,to ya aikata hakan" ABU DAWUD Malamai sun
yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin
mace lokacin da ya je neman aure
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne
kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da
take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta
juya baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum
zai san yanayin matar da zai aura.
Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa
aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga
ciki :
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai
KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a
rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda
ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali
ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai

15
in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan
yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman
aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a
iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yii dalilin aure, saboda in
namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna
ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a
cikin aikinta.
Allah shi ne ma fi sani.
25-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

13. INA CIKIN IDDA, SAI WANI YA YI ZINA DA

NI
Tambaya :
Malam mijina ya sake ni, bayan na yi tsarki daya, sai rikici ya
kaure tsakanin arna da musulmai a garinmu, sai wani christa,
ya dauke ni ya yi zina da ni, yanzu malam yaya zan yi game
da idda ta?
Amsa :
To 'yar'uwa ina rokon Allah ya kawowa musulmi dauki a
Nigeria, wannan mas'alar ta ki malamai sun yi sabani
akanta, akwai malaman da suka tafi akan dole sai kin yi
istibra'i bayan kin gama idda, saidai maganar da tafi zama
daidai ita ce : kawai za ki karasa iddarki ne, ba sai kin yi
istibra'i ba bayan kin kammala, saboda babbar manufar
istibra'i ita ce kubutar mahaifa, hakan kuma zai tabbata idan
16
kika karasa jinane biyun da suka rage miki na iddarki. Yana
daga cikin saukin addinin musulunci kasancewar duk
ibadojin da za su iya shiga cikin juna kuma manufarsu daya
ce, jinsinsu guda ne, to daya za ta shiga cikin daya, kamar
wacce ta yi jima'i sai kuma haila ta zo mata, wanka guda
daya ya ishe ta a karshen hailarta.
Domin neman karin bayani duba: Majmu'ul fawa'id na Sa'ady
shafi na: 141.
Allah ne mafi sani.
25-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

14. INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA


YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME?
Tambaya :
Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura
kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome,
amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki,
ko kuma na kyale shi na yi aurena? saboda gaskiya ina son
wancan, amma kuma ba na so na sabawa sharia ?
Amsa :
To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa
kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta :228, a
suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi
mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan
ta, amma zai iya shiga cikin manema. Idan ya yi da'awar
cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata

17
ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gaskata shi ba,
sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar
hakan. Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar da
za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake
kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan
yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za'a gaskata shi,
idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta . Saidai
wasu malaman suna cewa : idan har matar ta gaskata shi, to
ya isa, ko da bai kawo shaidu ba . Duba: Al-mabsud 2\23 da
Mawahibul-jalil 5/408
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
25-12-2014

15. IDDAR MATAR DA AKA SAKA SHIKA NA

UKU
Tambaya :
Sheik shin dole ga matar da mijinta ya yi mata shika uku sai
ta yi jini uku, ko idan ta yi jini daya ya yi, tun da babu kome?
Amsa :
To dan'uwa Mazhabar dukkan manyan malaman fiqhu shi ne
za ta yi jini uku ne, ko tsarki uku, saboda fadin Allah a cikin
suratul Bakara aya ta : 228 "Kuma matan aka saka, to za su
jira tsawon jinane uku", wannan ayar ba ta bambance
tsakanin matar aka saka shika daya ba, da wacce aka saka
saki uku, don haka sai hukuncin ya zama daya, Jassas yana
cewa babu sabani a cikin hakan.

18
Saidai Ibnu Taimiyya ya hakaito wani kauli wanda yake cewa:
za ta yi jini daya ne tun da babu kome, saboda an shar'anta
yin jini uku ne don tsawaitawa miji lokacin yin kome, tun da
kubutar mahaifa tana tabbata da yin jini daya. Wannan kaulin
ya sabawa zahirin ayar da ta gabata, sannan kasancewar
iddar matar da mijinta ya mutu wata hudu da kwana goma,
yana nuna cewa, ba saboda tsawaita lokacin kome kawai aka
shar'anta idda ba, tun da ita babu wanda zai mata kome.
Don neman karin bayani duba: Ahkamul-qur'an na Jassas
2/67, da kuma Ahkamul-qur'an na Ibunl-araby 1/185 da
Majmu'ul fatawaa 32\342.
29-12-2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

16. HUKUNCIN AIKIN JARIDA GA MATAR AURE


Tambaya:
Salam. Ina yiwa malam fatan alkhairi, Don Allah malam wata
Tambaya na zo da ita !, Ina hukuncin aikin jarida ga matar
aure ??
Amsa:
To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya umarci matar aure da
ta zauna a gidanta, kada ta fita sai in tana da wata bukata
mai muhimmanci, kamar yadda aya ta : 33 a suratul Ahzab
take nuni zuwa hakan.
Aikin jarida aiki ne da yake bukatar cakuduwa tsakanin maza
da mata, saboda mai aikin jarida za ta iya zama mai dauko
rahoto, wanda dauko rahoto yana lazimta haduwa da maza,
kamar yadda za ta iya haduwa da wanda ba muharraminta

19
ba, wajan hada wani shiri da za ta gabatar, wanda hakan zai
iya kaiwa zuwa barna, domin duk lokacin da mace take
kadaita da namiji to Shaidan zai iya shiga tsakaninsu.
Lalura tana iya halatta abin da yake haramun, saidai anan
wurin babu lalurar saboda za ta iya samun wani aikin na
daban wanda za ta tallafawa rayurwarta da shi, sannan maza
za su iya gamsarwa wajan aikin jarida, ta yadda zai zama, ko
da mata ba su shiga ba, aikin zai ta fi daidai. Aikin Jarida a
gidan talabishin hanya ce da wani zai iya ganin matar aure ya
yi sha'awarta, saboda duk wacce take gabatar da shirye-
shirye dole ta yi kwalliya, wanda hakan zai iya kaiwa zuwa
barna, ka ga sai ya zama haramun.
Malamai suna cewa : Duk lokacin da aka samu aikin jarida
mai tsafta wanda bai sabawa ka'idojin sharia ba, to ya hallata
mace ta yi, saboda duk hukuncin da aka haramta shi saboda
wata illa, yana zama halal idan ta gushe, saidai da kamar
wuya a samu hakan a irin kasashen da ba'a aiki da shari'ar
musulunci, wannan yasa barin aikin ga mace shi ne daidai,
musamman na talabishin wanda ya kunshi barna mafi gima,
kamar yadda bayani ya gabata. Allah ne mafi sani Don
neman Karin bayani duba : Al-mar'atu Almuslima Almu'asirah
na Ahmad Ba-badin shafi na : 429.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
4/2/2015

20
17. TSAKANIN KAFIRI DA MACE MUSULMA, WA ZAN

ZABA?

Tambaya:
Assalamu Alaikum. Na karanta post din da kayi akan
Shugabancin Mata, inda ka nuna bai halatta mace ta yi
shugabanci ba in ba na gidanta ba, Ina so ka dan yi mana
Karin bayani idan aka samu takarar shugabanci tsakanin
Kafiri da kuma Mace Musulma, wanne ya kamata mutane su
zaba a matsayin Shugaba?
Amsa :
To dan'uwa amsa wannan tambayar yana da wahala,
saboda ban ga littafin da ya tattauna mas'alar ba, amma dai
na nemi taimakon Amsa tambayar wajan babban
malaminmu Prof. Muhd Sa'ad Al-yuby, don haka ga bin da zan
iya cewa: Farko dai zaben kafiri haramun ne, saboda fadin
Allah madaukakin sarki "Kuma Allah bai sanya wata hanya ba
ga kafirai akan muminai" Nisa'i aya ta : 141, hakan sai ya
nuna bai halatta musulmai su sanya kafiri ya mulke su ba,
Kamar yadda zaben mace a matsayin shugaba shi ma
haramun ne saboda hadisin Abu-bakrah inda Annabi s.a.w.
yake cewa ; "Duk mutanen da suka sanya mace ta zama
shugabarsu, to ba za su rabauta ba" kamar yadda Bukhari ya
rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 4425, Ibnul-kayyim yana
cewa: kore rabauta dalili ne da yake nuna haramcin abu.
Bada'i'ul-fawa'id 4/812.
Saidai kamar yadda malaman shari'a suke cewa: duk lokacin
da abubuwa biyu haramtattu suka hadu, ya zama dole sai an

21
aikata daya daga ciki, to sai a dauki wanda ya fi saukin
haramci a aikata. Idan muka kalli manufar shugabanci a
musulunci, za mu ga ta kunshi: jagorancin mutane da kuma
tsayar da addini, wannan manufar za ta fi tabbatuwa idan
aka zabi mace musulma, fiye da kafiri Crister. Don haka
mutukar matar tana da kokari wajan addini, to ita ya fi
kamata a zaba, ba don kasancewar ya halatta a zabe ta ba,
sai don kawai hakan ya fi saukin haramci, kuma babu yadda
za'a yi a zauna babu shugaba.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
March 2015

18. WAI ME YASA MUSULUNCI YA HANA MUSULMA


AURAN CRISTA, AMMA YA HALATTAWA MUSULMI
AURAN CRISTA ?
Tambaya:
Malam wasu Arna ne suka mana tambaya a makaranta
cewa: Yaya aka yi addinin musulunci ya halattawa namiji
musulmi auran crister mace, amma ya hana a baiwa crister
namiji auran musulma, malam mun rasa Amsar da za mu ba
su, shi ne muke so ka taimaka mana, don kar su samu hanyar
da za su aibanta addininmu.
Amsa : To yar'uwa sheik Addiyya mohd Salim ya yi kokari
wajan warware wannan mushkilar a karashen tafsirin
Adhwa'ul-bayan da ya yi, inda ambaci dalilai guda biyu,
wadanda suka hukunta hakan:
1. Kasancewar musulunci shi ne yake yin sama, amma ba'a
yin sama da shi, idan crister ya auri musulma, zai zama yana
22
sama da ita, tun da namiji shi ne yake bawa mace umarni,
idan ya aure ta, sabanin idan namiji musulmi ne ya auri mace
crister, tun da shi zai zama a samanta .
2. Musulmi ya yi imani da Annabi Isa da kuma Injila, wannan
zai sa idan ya auri cristar zai girmamata, Shi kuwa crista bai
yi imani da Annabi Muhammad s.a.w. ba, don haka zai iya
wulakanta musulma idan ya aure ta, tun da bai san darajar
addinita ba, wanda hakan zai kai suka sa fahimtar juna,
zaman auran ya ta'azzara. Duba Adhwa'ul-bayan 8/164
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
13/2/2015

19. JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKE


Tambaya :
Assalamu Alaikum Malam matata ta haihu sati biyu kenan, to
Malam yanzu takan wuni Jini bai zoba sai da Daddare in ta
kwanta sai Jinin yazo. To shin Malam za ta iya yin
wanka/tsarki da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i? Kokuma
yaya zatayi? Nagode Allah Yaqara illimi mai albarka.
Amsa:
To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to
yana daukar hukuncin jinin biki ne , haka ma tsarki yana
daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk
yinin da ba ta ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-
kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta
ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci
akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "Bai sanya muku

23
kunci a cikin addini ba" Suratu Hajj 78. Don neman Karin
bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1/214.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
22/2/2015
20. JINI YA ZO MIN, BAYAN CIKINA YA KAI WATA
BIYU
Tambaya:
Assalamu alaikum, malam ya kokari malam tambayace
gareni, na yi wata biyu ban ga al'ada ba, sai yanzu ta rinka
zuwa tana daukewa, na zo asibiti sun ce juna biyu ne, to
inyazo min da safe shikenan sai ya dauke sai kuma gobe da
safe, sai in ya dauke inyi wanka in cigaba da sallah, malam to
ko ya halatta hakan?
Amsa:
To yar'uwa wannan jinin da kika gani mutukar yana kama da
jinin hailar da kaki saba gani, to zai hana sallah, kuma zai
dauki dukkan hukunce-hukuncen jinin haila, saboda asali duk
jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai ba
akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba, kuma
babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi ya
zama haila.
A zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila, don haka duk
yinin da ki ga jini to yana daukar hukuncin jinin haila ne ,
haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta
yadda za ki yi wanka duk yinin da ba ki ga jini ba, Saidai idan
yana yayyankewa kusa-kusa, to kina iya jinkirta wankan, sai
ki hada sallolin da ba ki ga jini ba a lokutansu, saboda yin
wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah
24
yana cewa : "Bai sanya muku kunci a cikin addini ba" Suratu
Hajj 78. Don neman Karin bayani duba Almugni na Ibnu
Khudaamah 1\214 da Dima'uddabi'iyya shafi na 11
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
26/2/2015

21. MAHAIFIYATA TANA ZUWA WAJAN BOKA, INA


NEMAN SHAWARA
Tambaya: Assalamu alaikum don Allah malam a fitar dani
cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta
je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake
damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun
yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri
aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife
abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu
bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar
kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata
bata aminta da malaman bane, shi yasa na keso ka bani
fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a
addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zanbi wajen kin
biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda inada matsala, ta
bangaren aqida mun banbanta? Wassalam nagode Allah ya
qara basira.
Amsa :
To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai
ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu
malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta
hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da
25
Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai
kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da
aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a
ruwan da aka zuba magarya guda bakwai. Amma bai halatta
ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya
nema ba, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon
Allah. Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita
cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
yana cewa :" "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi
wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in"
kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230.
Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai
matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta
yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa : "Duk wanda ya
je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya
kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi" kamar
yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904,
kuma Albani ya inganta shi .
INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR
DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
8/3/2015

22. MIJINA BA YA SALLAH, KO ZAN IYA NEMAN YA


SAKE NI?
Tambaya:
Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira,
malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da

26
mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin
Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da
ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana
saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun
ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki
tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi?
na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.
Amsa :
To 'yar'uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki
iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a
zance mafi inganci, kamar yadda Annabi s.a.w. ya fada a
hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81. Ga shi kuma
aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin
musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala
a addinance. Allah ya hana saduwa da mace mai haila a
suratul Bakara ayata: 222, Saduwa da mace da rana a
Ramadana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari
mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan. Saidai zunubin barin
sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba,
za ki iya kai shi kotu, alkali ya rabaku. Don neman Karin
bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
6/3/2015
23. ZAN AURI KANWAR MATAR MAHAIFINA, KO
YA HALATTA?
Tambaya:

27
Malam ya halata mahaifina ya aure mace, ni kuma na auri
kanwarta.
Amsa:
To dan'uwa ya halatta ka aureta, saboda ba ta cikin mataye
guda goma sha biyar wadanda Allah ya haramta a aure su a
cikin suratun-nisa'ai, ga shi kuma babu wani hadisin da ya
haramta a aure ta, Allah yana cewa a cikin suratunnisa'i aya
ta: 24, bayan ya ambaci matan da aka haramta a aura, "Duk
matan da ba wadannan ba, to an halatta muku ku aure su.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
10/3/2015

24. BUDURWATA BA TA HAILA, FALALACE KO MATSALA


CE?
Tambaya:
Assalamu alaikum dan Allah malam a taimaka min, matar da
zan aura a yanzu haka auren bai fi wata biyu ba, shekararta
20 amma ba ta taba jinin haila ba. To malam wannan
matsalace ko kuma falalace ? sannan kuma za ta iya
haihuwa? MALAM A TAIMAKAMIN DON ALLAH (S.W.T).
Amsa:
To dan'uwa tabbas haila tana daga cikin alamomin da suke
nuna cewa mace za ta iya daukar ciki, kamar yadda wasu
malaman tafsirin suka fada, wannan ya sa lokacin da za'a
yiwa matar annabi Ibrahim bushara da haihuwa, sai da ta yi
haila, saboda kasancewarta tsohuwa, haila kuma alama ce ta
haihuwa, don haka duk matar da ba ta yin haila da wuya ta
haihu.

28
Akan iya samun wasu matan 'yan kadan wadanda suke iya
haihuwa ko da ba su taba yin haila ba, saboda Allah mai iko
ne akan komai. Abin da nake ba ka shawara shi ne ku je
wajan likitoci, don su gwada ta, in har suka tabbatar ba za ta
iya haihuwa ba, kana iya hakura da auranta, saboda haihuwa
ginshiki ne, daga cikin ginshikan da suke sa ayi aure. Rashin
yin haila ba falala ba ce, saboda hadisi ya tabbatar da cewa :
"Haila jini ne da Allah ya hukuntawa dukkan 'ya'yan nana
Hauwa'u da jikokinta" kamar yadda Bukhari ya rawaito a
hadisi mai lamba : 290. Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
11/3/2015

25. MACE ZA TA IYA YIN LIMANCI?


Tambaya :
Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace tai wa
mata yan'uwanta limanci toh in ramadan ya zo na kan tara
mata na musu, dayake duk anguwan na dan fi su karatu, toh
kusan anguwan ba malamin sunna ko daya sai 'yan bidi'a, shi
ne suke nema na ba su aya ko hadisi akan hakan malam,
ataimakamin don Allah?
Amsa :
To 'yar'uwa ina rokon Allah ya jikan malam Ja'afar, mu kuma
ya kyautata namu karshen, ya halatta mace ta yiwa
'yan'uwanta mata limanci, saboda abin da aka rawaito cewa :
Nana A'sha da Ummu Salama –Allah ya kara musu yarda- sun
yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin

29
Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan nan Shafi'i a
Musnad dinsa da sanadi mai kyau, Almajmu'u (4/187).
Haka nan an rawaito cewa Annabi s.a.w. ya sanyawa Ummu-
waraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yiwa matan
gidansu limanci, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi
mai lamba ta : 491, kuma Albani ya kyautata shi.
Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yiwa matan unguwarku
limanci, tun da kin fi su karatu, Annabi s.aw. yana cewa:
"Wanda ya fi iya karatun alqur'ani shi ne zai yi limanci"
Muslim 1078. Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a
tsakiyarsu in suna da yawa, in kuma ita kadaice sai ta tsaya a
damarki.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
13\3\2015
26. NA SADU DA IYALINA, INA AZUMIN NAFILA!
Tambaya :
Salam malam ina hukuncin wadda yana azumin nafila, sai
sha'awa ta zo mai sai ya karya kuma ya sadu da matarsa?
Amsa:
To dan'uwa malamai sun yi sabani game da wanda ya sadu
da matarsa, alhalin yana azumin nafila, akwai wadanda suka
ce sai ya sake, saboda ya bata aikinsa wanda ya faro, kuma
Allah yana cewa: "Kada ku bata ayyukanku" Muhammad aya
ta: 33.
Akwai malaman suka tafi akan cewa ba zai sake azumin ba,
kuma ba shi da laifi. Wannan maganar ta karshe, ita ce
daidai, saboda Annabi s.a.w. yana cewa: "Mai azumin nafila

30
sarkin kansa ne, in ya ga dama ya cigaba da azumi, in ya ga
dama kuma ya karya" Albani ya inganta shi a sahihul-jami'i
hadisi mai lamba ta: 3854. Wannan hadisin sai ya nuna ba shi
da laifi idan ya karya, karya azumi yana tabbata da cin abinci
ko abin sha, ko jima'i, Don neman Karin bayani duba Tuhfatul-
ahwazy 3/356.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
16/3/2015

27. INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN

BUDURWATA ?
Tambaya:
Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da nike so in aura?
Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaman bayanin abunda
ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin muyi aure.
Na gode. Allah ya gafarta maka.
Amsa :
To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura,
kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake
cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar
kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan"
Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082. Malamai sun yi
sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace
lokacin da ya je neman aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne
kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace,

31
kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita
akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai. 2.
2. Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka
bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.
3. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da
take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta
juya baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa,
saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura,
yadda ya kamata. Saidai ba'a son yawaita kallon saboda
duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a
tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance
da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana
iya tayar da sha'awa, sha'awa tana iya kaiwa zuwa barna.
Don neman Karin bayani, duba: Al'insaf 8/15 da Muhallah
9/161.
Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa
21/3/2015

28. MATATA TANA NAKUDA, GA SHI KUMA AN TADA


SALLAR JAM'I
Tambaya:
Wani ne a office ana kiran shi a waya, matarshi na
matsanancin hali na naquda, ana buqatarsa, ikon Allah kuma
gashi an tada iqama za'a yi sallah sai wasu suka ce ya tafi
wurin mara lfy. Wasu kuma suka ce ya tsaya ya gama sallar,
me ya kamata ya yi ?
Amsa :
To dan'uwa abin da yake daidai anan Shi ne : ya tafi wajan
matarsa, saboda idan hakkin Allah da na bayi suka ci karo,

32
akan gabatar da na bayi, saboda shi Allah mawadaci ne.
Sannan za ta iya hallaka idan ka bar ta ba ka je ba, sallar
jam'i kuma akwai sabani akan wajabjinta, ga shi kuma za ka
iya gamawa ka dawo kafin lokacinta ya fita, yana daga cikin
ka'idojin sharia, duk abin da ake bukatarsa yanzu-yanzu akan
gabatar da shi akan wanda za'a iya jinkirtawa, ko da bai kai
shi daraja ba.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
22/3/2015

29. ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA


TSORON CIN HARAM?
Tambaya:
Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani
ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa
za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene
halarcin auransa a shari'a? Saboda tana tsoron kar ya rika
ciyar da ita da dukiyar haramun.
Amsa :
To dan'uwa Annabi s.a.w. yana cewa: "Allah ya la'anci mai cin
riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka"
Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598. Hadisin da
ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke
mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko
kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin
banki, kamar mai gadi, da dan aike. . Duba fatawaa Allajanah

33
adda'imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin
2/401.
Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa haramun
ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a
auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun Malamai
suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin
halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa, saboda
Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a
dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata
sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa ba.
Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin
ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
10\4\2015

30. SHIN ABAYA TANA DAUKAR HUKUNCIN HIJAB?


Tambaya:
Assalamu alaikum, Malam don Allah tambaya nake da ita
kamar haka: Abaya da mata suke sanyawa tana iya daukan
hukuncin Hijabi ne, domin zaka ga ko harami za ka gan su da
irin wannan shigar, kuma nayi kokarin leka wasu littafai masu
alaka da hijab ban iya kaiwa ga magana akan hakan ba.
Malam ko akwai maganganun malamai akai? Allah ya saka
maka da alkhairi.
Amsa:
To dan'uwa, abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne : ta
sanya tufan da zai suturce jikinta, in ban da fuska da tafin
34
hannu a wajan wasu malaman, wasu malaman kuma suna
ganin fuska al'aura ce, don haka ita ma ya wajaba a rufe ta,
tun da a nan kyawun mace yake, kayan da za ta sa su zama
masu kauri, ba ya halatta ta yi ado in ba a cikin gidan mijita
ba, ko tare da muharramanta. Suturar mace musulma ba'a so
ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba'a so su zama
kayan da za su ja hankali, ko wadanda aka fesa musu turare ,
Mutukar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata,
ba ta matse shi ba, za ta dauki matsayin hijabin da Allah da
manzonsa, suka yi umarni.
Don neman Karin bayani duba : Majmu'ul-fataawa 22/110 da
Hijabul- mar'atulmuslima shafi na : 54 zuwa 67.
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
15/4/2015

31. LAULAYIN CIKI YASA INA WAIWAYE A SALLAH,


YAYA SALLATA?
Tambaya :
Assalamu alaikum malam Dan Allah macece take fama da
yawan zuban yawu a bakinta na laulayin ciki, Wanda yakai
kafun nayi raka'a daya ya cikamun baki sai na dan juya in
zuba akan tsumma, sallan yayi ko bani da halin juyawa kadan
?
Amsa :
To 'Yar'uwa Annabi s.a.w. yana cewa : "Waiwaye a sallah wani
faucewa ne da Shaidan yake fauta daga sallar bawa" kamar
yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lambata : 718.

35
Malamai suna cewa waiwaye a sallah makaruhi ne saboda
hadisin da ya gabata. Waiwaye yana halatta idan akwai
bukata, saboda akwai lokacin da sayyidina Abubakar ya fara
limanci, saboda Annabi s.a.w. baya nan, bayan Annabi s.a.w.
ya dawo sai ya shigo masallaci, sahabbai suna ganinsa sai
suka fara tafi, sai sayyadina Abubakar ya waiga lokacin da ya
ji tafi ya yi yawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi
mai lamba ta : 2544.
Malamai suna cewa : waiwayan da Abubakar ya yi yana nuna
hallacin yin waiwaye saboda bukata, tun da Annabi s.a.w. bai
masa inkari ba. Don neman karin bayani duba : Fataawaa
nurun Aladdarb 9/225.
A bisa abin da ya gabata, ya hallata ki dinga yin waiwaye
saboda zubar da yawun da ya zama lalura, saidai duk abin da
aka halatta saboda bukata, ba'a so a wuce gwargwadonta .
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
19/4/2015

32. ZAN IYA KARA GASHI, SABODA MIJINA?


Tambaya :
Malam na yi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana
bakin ciki, in ya ga kaina, zan iya kara gashi, don zaman
auranmu ya kara dadi?
Amsa:
To 'yar'uwa wata mace ta je wajan Annabi s.a.w. ta ba shi
labari cewa: 'Yarta ta yi rashin lafiya gashinta ya fadi, kuma
gashi mijinta ya umarceta da ta kara mata gashi, shin za ta

36
iya karawa? sai Annabi s.aw. ya ce mata : A'a, saboda an
la'anci masu kara gashi" Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai
lamba ta: 4831 .
Hadisin da ya gabata, yana nuna cewa : bai halatta mace ta
kara gashi ba, ko da kuwa mijinta ne ya umarceta, saboda
hakan zai sa ta shiga tsinuwar Allah .
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
22/4/2015

33. INA SON DALILI AKAN WAJABCIN SANYA


SAFAR KAFA GA MACE ?
Tambaya :
Assalamu alaikum, malam ina son in san wajibcin sanya
safar kafa (socks) ga mace. Nagode
Amsa :To 'yar'uwa da yawa daga cikin malamai suna
wajabtawa mace rufe duga-duganta, suna ganin yana daga
cikin al'aura. Saidai Abu-hanifa yana ganin ba shi daga cikin
al'aura, hukuncinsu daya da fuska da tafin hannu, ya dogara
da fassarar da wasu sahabbai suka yiwa aya ta : 31 a
suratunnur, inda Allah yake cewa: "Kuma kada su bayyana
adonso sai abin da ya bayyana", inda suka fassara abin da ya
bayyana da fuska da duga-dugai, da tafin hannu.
Ummu Salma ta kasance tana tsawaita suturarta, ta yadda
take jan kasa, kamar yadda Malik ya rawaito a Muwadda'i a
hadisi mai lamba ta: 4547. Don haka har a wajan wadanda
suke ganin wajabcin rufe duga-dugai, to za ki iya rufewa da
doguwar rigarki, ba dole sai kin sanya safa ba. Don neman

37
Karin bayani duba : Al-mabsud 10\153 da Majmu'ul fataawa
22/114 .
Allah ne ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
27\4\2015

34. NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE


SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO
AKWAI DAMAR KOME?
Tambaya :
Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana
wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya
sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu
shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake
biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa
shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a
tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya
mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika
nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai
naji daga gareka
Amsa :
To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to
babu damar kome, sai in ta auri wani mijin na daban, saboda
igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu . Auren
da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta
auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta,
da ba'a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin

38
maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani ba, ya
wajaba ku hakurewa juna.
Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu-Khudaamah
7/388 .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
3/5/2015

35. YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN


MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?
Tambaya :
Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki
matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su ba
har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su
yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?
Amsa :
To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za
su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci
gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne,
Ibnu-khudamah ya hakaito ijma'in malamai akan haka. Don
neman Karin bayani duba : Al-mugni 8/94.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
9/5/2015

36. MATA ZA SU IYA YIN SALLAR JANA'IZA?


Tambaya:
Salam, malam ya halatta mata su bi sallar jana'iza ? saboda
na ga wani malami lokacin da aka kashe masa ‘yaya har
mata ya tara aka yi musu sallar jana'ixa Ngd malam
39
Amsa:
To dan'uwa ya halatta mata su yi sallar jana'iza, saboda
dalilan da suka zo akan sallar jana'iza ba su banbance
tsakanin mace da namiji ba.
Duk nassin da ya zo daga Al'qur'ani ko sunna, to yana hade
maza da mata wajan hukunci, in ba'a samu wani dalili ko
alama wacce ta fitar da su daga ciki ba . Sannan mata
sahabbai sun yiwa Annabi s.a.w. sallah bayan ya mutu, babu
kuma wanda ya yi inkarin hakan, sai wannan ya nuna shi ne
shari'a.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
11/5/2015

37. INA SON DALILI AKAN KACIYAR MATA ?


Tambaya :
Assalamu alaikum, don Allah malam a taimaka min da amsar
wannan Tambayar, ko Qur'ani da hadisi sun yi Magana akan
halarcin kaciyar mata, ko kuma wani daga cikin magabata na
kwarai ya yi Magana akan haka ?
Amsa :
To 'yar'uwa akwai hadisai da suka zo akan cewa : mustahabbi
ne, yin kaciyar mata, saidai an yi sabani akan ingancinsu,
wasu malaman sun raunana su, wasu kuma sun inganta su.
Baihaki a Sunanu Assugrah a hadisi mai lamba ta : 3712, ya
rawaito mustabbacin yin kaciyar mata daga Ibnu Abbas da
sanadi mai kyau.
Hadisin da Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a lamba ta :
108, daga Nana A'isha tana cewa : "Idan kaciya ta hadu da

40
kaciya, to wanka ya wajaba" na nuna cewa : al'ada ne yiwa
mata kaciya a zamanin Annabi s.a.w.
Ibnu- Abi-zaid Al-kairawany ya ambata a Risala shafi na : 410,
cewa : yin kaciyar mata mustahabbi ne. Don neman Karin
bayani duba Al-mugni 1\101.
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
12/5/2015

38. 'YAMMATAN DAJIN SAMBINSA, ZA'A IYA ZUBAR


DA CIKIN DA SUKA DAUKO?
Tambaya: Don Allah Shehi me za Ku ce game da yanayin
mata masu ciki
ta hanyar fyaden Yan Boko Haram, wadanda aka kwato su a
Sambisa. Muna bukatar nusarwa a shariance game da me za
a yi da cikkunansu. A zubar Ko a Bari. Idan za mu samu
amsa a mafi kusancin lokaci za mu so haka. Na gode.
Amsa :
To dan'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu :
1. Idan ya zama cikin na zina ba'a busa masa rai ba, kamar
ya zama bai kai kwanaki 120 ba, to wannan malamai sun yi
sabani akansa zuwa maganganu uku : A. Wadanda suka tafi
akan halaccin zubar da shi, saboda bai zama mutum ba,
kuma in an haife shi zai zama aibi ga uwarsa, shi ma kuma ba
zai yi rayuwa mai dadi ba.
B. Bai halatta a zubarba, saboda Annabi S.A.W bai umarci
Gamidiyya da tayi zina ba, ta zubar da cikinta, cewa ya yi da
ita: ta je ta haife, sai ta zo a tsayar mata da haddi, kamar
yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1696.
41
C. Akwai malaman da suka tafi cewa: idan fyade aka mata,
za'a iya zubarwa, mutukar ba'a busa rai ba.
2. Idan ya zama bayan an busa masa rai, wannan kam bai
halatta a zubar ba, saboda kashe rai ne, wanda bai ji ba bai
gani ba, yana daga cikin manufofin sharia kiyaye rayuwar
dan'adam. Zance mafi inganci shi ne bai halatta a zubar da
cikin zina ba ko da ba'a busa masa rai ba, saboda hakan zai
iya bude hanyar yaiwaita zinace-zinace, tun da za'a iya zubar
da cikin ba tare da an shiga cikin kunci da kunyata ba, amma
idan Fyade aka yi mata, ko kuma likita ya tabbatar da cewa
za ta halakka idan ta cigaba da zama da cikin, to ya halatta a
zubar a irin wannan lokacin. Matukar an busawa ciki rai bai
halatta a zubar ba, ko da kuwa fyade ne. Don neman Karin
bayani duba Ahkamul-janin Fil-fiqhil Islamy na Umar Ganam.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
16\5\2015
39. BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN
MAGANIN HANA HAILA?
Tambaya :
Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na
sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani
yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce
min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan
tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske ?
Amsa :
To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta,
Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya

42
haramta saboda fadin Allah “Kar ku jefa kawunanku a cikin
halaka” suratu Albakarah aya ta 1952.
Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka
gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta
taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa
kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa,
musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna
dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai
a kiyaye.Don neman karin bayani, duba : Dima'uddabi'iyya
shafi na: 54 .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
22-6-2015

40. YA SAKI MATARSA SAKI UKU, AMMA BAI GAYA


MATA, SHIN TA SAKU ?
Tambaya :
Assalamu alaikum Allah Ya gafarta Malam mutum ne ya saki
matarsa saki daya. Da yayansa yaji labari sai ya kira shi yake
masa fada ya nemi akan lallai ya mayar da ita. Sai kawai ya
gayawa yayan nasa cewa saki uku yayi mata alhali saki daya
yayi, ya fadi hakan ne saboda ba yaso a tilasta masa ya
mayar da ita. To Malam shin menene matsayin wannan
maganar da mijin yayi na cewa saki uku yayi wa matarsa
alhali saki daya yayi mata?
Amsa :
Ta saku saki uku, saboda ba'a wasa da saki, kamar yadda
Annabi s.a.w, ya fada, sannan kuma ya tabbatar da cewa :
43
Allah yana afuwa ne game da zancen zuci, amma abin da aka
furta yana da hukunci. Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
24-6-2017

41. ZAN SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR AIDS?


Tambaya :
Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce
tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da
ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su
da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe
mu, amma ina neman shawara ?
Amsa :
To dan'uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi,
wadanda ba'a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci,
saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar'anta saki
wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin
ma'aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta,
tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai hadari
kuma ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda
wannan dalilin, tun da malaman Fiqhu sun halatta raba aure
saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul
Jalil Sharhu Muktasarul Khalil : 6\478 Cutar Sida kuma tafi
kuturta tsanani. Sannan ba za'a kalli cutuwar da za ta yi ba,
bayan an saketa, domin yana daga cikin ka'idojin Sharia : kau
da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar
da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki

44
cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za'a waiga
zuwa damuwarta ba a nan wurin. Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
30/8/2015

42. ZAN IYA NEMAN SAKI SABODA MIJINA BA YA


HAIHUWA?
Tambaya: Don Allah malam na auri wani mutum, amma har
yanzu ba mu haihu ba, shin zan iya neman saki, don na ji an
ce Annabi s.a.w. ya ce matar da ta nemi saki ba za ta shiga
aljanna ba?
Amsa :
To Yar''uwa hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w. cewa : "Duk
matar da ta nemi saki ba tare da wani dalili ba, ba za ta ji
kamshin aljanna ba" kamar yadda Abu-Dawud ya rawaito a
hadisi mai lamba ta : 2226. kuma Albani ya inganta shi.
Wasu malaman sun tafi akan cewa mace za ta iya neman
saki, idan ba ta san mijinta ba ya haihuwa ba, sai bayan sun
yi aure, saboda wannan yana iya zama aibun da za'a iya raba
aure saboda shi,. Duba : Sharhul-mumti'i 12/ 220.
Saidai zai yi kyau kada ki yi gaggawar rabuwa da shi, saboda
a lokuta da yawa, Allah yana iya jarrbar miji da rashin
haihuwa, daga baya kuma sai Allah ya warware masa ya
bashi 'ya'ya .
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
1\9\2015

43. SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?

45
Tambaya:
Salam malam yayata ta jidda ta ce in tambaye ka menene
hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan
bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma
wai don Allah ka Amsa a facebook, saboda ana bukatar sanin
amsar.
Amsa:
To 'yar'uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta
yiwa wani dawafi, sannan kuma ba'a samu magabata na
kwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma
ibada ba'a yin ta sai da dalili daga Alqur'ani ko Sunna, amma
dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake yiwa
kansa dawafi.
Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin yiwa
wani Umara ko Hajji, saidai ba'a samu na dawafi a karan
kansa ba.
Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda
dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne
da suka hada jiki da dukiya, duk ibadar da ta hada jiki da
dukiya, tana Amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki
kawai ba ta Amsar wakilci kamar sallah.
Allah ne mafi Sani
7-9-2015
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

44. SHIN YA HALATTA MATAR AURE TA YI


FACEBOOK?
Tambaya :

46
Assalamu alaikum, shin ko ya halatta ga matar Aure ta yi
facebook, harma da charting?
Amsa : Wa alaikum assalam Wannan tambaya ce mai
wahala. Saidai abin da zance duk abin da zai amfane ta za ta
iya yi a face book, saboda asali a shari'ar musulunci, duk abin
da mutane suke aikatawa a mu'amalarsu ta yau da kullum
halal ne, mutukar ba'a samu wani nassi wanda ya haramta
ba, ko kuma ya kasance cuta tsantsa, haka ma idan mafi
rinjayansa barna ne, ka ga face book kuwa babu wani nassi
da ya haramta shi, sannan ba cuta ba ne tsantsa, tun da ana
iya samun ilimin addini ta wannan kafa. Ya kamata ta daina
yin charting da wadanda da muharramanta ba in ba malamin
da ta yadda da iliminsa da tsantseninsa ba, za ta yi masa
fatawa, saboda akwai maza da yawa da suke bi ta hanyar
charting don lalata matan auren da ba su da kamewa.
Wannan ya sa barin charting da mazan da ba muharramai ba,
ko kuma wadanda suke neman auran matar, zai iya zama
wajibi, saboda hakan yana kaiwa zuwa barna, duk abin da
yake kaiwa zuwa barna, zai iya zama haramun ko makaruhi,
kamar yadda malaman musulunci suka tabbatar.
Allah ne mafi sani
29-9-2015
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

45. NA AURI AMARE BIYU A RANA DAYA, YAYA


ZANYI WAJAN TAREWA?
Tambaya:
Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya auri mata biyu
(sangaya) rana guda, to dakin wacce zai fara shiga? Nagode
Allah ya karawa malam imani.

47
Amsa:
To dan'uwa wasu daga cikin malamai sun karhanta auran
mata biyu a yini daya, saboda hakan zai kawo matsala wajan
bawa matan hakkinsu na kwana, saboda duk wacce aka fara
da ita, to dayar za ta cutu, saidai idan hakan ta faru, to zai
fara ne da wacce ta fara shigowa gidan, in kuma sun shigo
tare ne sai ya yi musu kuria. Don neman Karin bayani duba :
Al-kafy Na Ibnu Khudaamah shafi na: 981. Allah ne ma fi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
5/10/2015
46. FATAWAR NAN AKWAI GYARA
Malam fatawarka da ka yi akan mijin da matarsa ta neme shi
da jima'i, bai amsa mata ba, ba shi da laifi, mun watsa ta a
group da yawa, kuma ta hadu da kalubale, ga abin da wata
take cewa: Nake ganin idan har aka ce namiji kawai ne zai
iya kusantar matarsa duk lokacin da ya so ko tana so ko ba
ta so, ita mace idan ta nemi hakan ko bai biya ma ta
buqatarta ba sai lokacin da ya so, Anya akwai adalci a
hakan? Idan akwai istidlali naqli a taimakamin da su ba aqali
ba. Na ga istidlal din na aqali aka kawo a rubutun.
Ya za'ayi mace ta nemi mijinta ya qi amince ma ta, duk da
kasancewar mace tana da kunya. Amma har ta iya nemansa
ka ga kuwa akwai dalilin da ya sa ta neme shi. Ai shi ma
namiji ko da bai da sha'awa da an taba shi sha'awarshi za ta
motsa. Kenan hakan ba zai zamo dalili da zai sa don mace ta
nemi mijinta ba ya ki amincewa da dalilin wai baya da
sha'awa.
Amsa:
To abin da zan iya cewa shi ne: saduwar da muke magana
akanta ibada ce, ibada kuma tana bukatar dalili kafin a
tabbatar da ita, babu wani dalili Wanda ya wajabtawa miji

48
amsa kiran matarsa duk lokacin da ta neme shi, sannan
yanayi da al'ada ya tabbatar da cewa namiji ba zai iya
saduwa da mace ba duk lokacin da ta name shi, saboda
Namiji yana bukatar nashadi kafin saduwa, sabanin mace,
wacce take a matsayin katifa, wannan yasa malamai da
yawa na sharia suka tafi akan cewa ba'a yiwa namiji fyade,
tun da in azzakarinsa bai motsa ba, ba zai sadu da mace ba,
mace kuwa an cimma daidaito za'a iya mata fyade saboda
kamar tirmi take, in har an samu tabarya shike nan, wannan
yasa za'a iya saduwa da mace tana bacci sabanin namiji.
Kasancewar an ce babu la'anta akansa idan matarsa ta
neme shi bai amsa mata ba, ba ya nuna ya halatta ya cutar
da ita, yaki saduwa da ita a lokacin da yake da nishadi. Allah
ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
14/10/2015

47. ZAN IYA ZUBAR DA CIKIN DA NA TABBATAR


SIKILA NE?
Tambaya:
Salam malam ni AS ce, mijina ma genotype iri daya muke
da shi, yarana biyu babban AA karamar AS, duk sanda na
sami chiki muna zuwa a duba mana genotype din babyn
dake chikin, likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a
chire, amma bai kaiwa 4months muke chirewa, mallam meye
hukunchin yin hakan ?
AMSA: Wa alaikumus salaam warahmatullahi wa
barakaatuhu, To 'yar'uwa

49
Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an
busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.
Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai
watanni hudu, wasu sun haramta, wasu sun halatta wasu
kuma sun karhanta.
Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin
da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin
Sikila ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa
ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin
cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata
hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya
fuskanta a rayuwarsa, ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai
zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.
Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fiqhil
islamy na Umar Ganam Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
18/10/2015

48. IN BA KI DAWO DA ABIN DA KIKA DAUKA BA, NA


SAKE KI
Tambaya: Assalamu alaikum Malam mutum ne matarsa ta
dauki abinsa, sai yace kodai ta dawo da abinda ta dauka ko
kuma ya saketa, ita kuma zafin wannan maganar da yayi, sai
tace ba za ta dawo da abin ba, sai yace ya saketa, sai tace
masa saki nawa, sai yace konawa take so, sai ta yi shiru ba
tace komai ba, sai yayi maza ya shedama mahaifinta abinda
ya faru, da cewa ya sata, ta maido da abin da ta dauka
domin ya warware kalamin da yayi, daga qarshe ta maido da

50
abin, malam matsalar anan shi ne matar tace ya saketa
amma shi yace bai sake tava , Allah ya san zuciyar shi , idan
harta dawo mashi da wannan abun ,to ya warware kalamin
sakin da yayi, matar ta tsayu akan saki ne amma shi yace ba
sakine va, Mallam don Allah menene gaskiyar wannan lamari
? Allah yasaka da alkhairi amin.
Amsa: Abin da yake daidai shi ne saki ne, saboda niyya ba
ta da tasiri a saki,
ana amfani ne da Abin da miji ya furta. Ya rataya sakin da
wani abu, kuma abin ya tabbata, ya kuma zo ya furta, don
haka ta saku. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
20/10/2015

49. YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA ?


Tambaya:
Ass. Malam shin mutum ya furta saki ga matarsa ba ta jiba,
shin ta saku ?
Amsa:
To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi
daga cikin sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta
saku koda ba ta ji ba, yana daga cikin ka'idoji a wajan
malaman fiqhun musulunci: Duk wanda ba'a damu da
yardarsa ba wajan tabbatuwar abu, ba'a damuwa da
saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajan zartuwar saki,
haka ma saninta an yi sakın ba sharadi ba ne wajan
tabbatuwarsa.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa

51
31/10/2015

50. MATAR DA TA GAYYATO JININ HAILA KAFIN


LOKACINSA, YAYA SALLARTA?
Tambaya:
Salam malam ina hukunchin macen da in mijinta ya fitine ta
da jima'i take shan magani don jini yazo mata, Yaya
hukuncin jinin yaya kuma maganar sallah, ? tunda gayyato
jinin ta yi.
Amsa:
To 'yar'uwa Allah da manzonsa sun rataya hukunce-
hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, kamar yadda aya ta:
222 a suratul-Bakara take nuni zuwa hakan, duk da cewa
gayyato shi ta yi saidai zai dauki dukkan Hukunce-hukuncen
haila, mutukar ya zo da siffofinsa. Gayyato jini saboda hana
miji jin dadi bai dace ba, saboda duk dabarar da za ta kai
zuwa haramun to ita ma ta zama sabon Allah, Ya wajaba ga
mace ta baiwa miji kanta duk lokacin da yake bukata, in ba
tana da uzurin da sharia ta yarda da shi ba, don haka bai
kamata mace ta hana mijinta saduwa da ita ba ta hanyar
dabara.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
31/10/2015

51. TA AURI WANDA BAYA IYA JIMA'I HAR SUKA RABU,


SHIN ZATA YI IDDA?
Tambaya:
Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri
kanwata, sai daga baya muka gane ya ha'incemu sakamakon
52
rashin mazantaka da baya dashi, daga baya da asirinsa ya
tonu sai ya saketa, shin malam za tayi Idda ne ? don babu
wata mu'amalar Aure da ya taba shiga tsakaninsu.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Mutukar ba su taba kwanciyar aure ba,
ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta : 49 a suratul
ahzaab take nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
21 Muharram, 1437 (03/11/2015)

52. MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASA BAYA?


Tambaya:
Assalamu alaikum, Allah ya hadani da miji mazinaci, shin in
na daina hada shinfida dashi dan gudun daukar wani ciwo
innada laifi?
Amsa:
Wa alaikum as salam, abin da ya fi shi ne ki yiwa
magabatansa bayani, don su tsawatar masa ya daina, in
Kuma kin tabbatar ya dau cutar aids kina da damar da za ki
je wajan alkali don ya raba auren, tun da musulunci ya yi
umarni da tunkude cuta gwargwadon iko, in har miji yana
ciyar da matarsa to ya wajaba ta amsa kıransa, wannan
yasa daukar matakin hana shi kanki zai iya jawo muku
rigima, sanya alkali ko magabaci a hukuncin shi ne daidai.
Allah shi ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Zarewa
21 Muharram, 1437 (03/11/2015).

53
53. ZAN IYA YIWA MATATA KOME, BAYAN TA FARA JINI
NA UKU?
Tambaya:
Malam idan mace tana iddah Har tana Kan jini na uku. miji
zai iya maida ta?
Amsa:
To Dan'uwa Allah yana cewa a suratul Bakara aya ta: 228,
"Kuma matan da aka şaki, za su jira (kur'i) uku kafin su gama
idda", saidai Malamai sun yi sabani game da ma'anar (kur'i)
a ayar.
A wajan malaman Malikiyya kur'i a ayar yana nufin tsarki,
don haka duk matar da aka saka in dai ta shiga jini na uku to
miji ba shi da damar yi mata kome, saboda za'a sake ta ne a
tsarki sai ta yi jini sai tsarki, sai jini sai tsarki, daga ta shiga
jini na uku za ta zama ta kammala iddarta.
Malaman Hanafiyya sun fassara (Kur'i) a waccar ayar da jini,
don haka mutukar ba ta kammala jini na uku ba, to miji zai
iya mata kome, Tunda zata fara idda ne da jini, don haka ba
zata kammalaba sai a karshen jini na uku.
Wasu Malaman suna inganta Mazahabar Hanafiyya saboda
Annabi s.a.w ya kira haila da sunan Kur' i a hadisin Imamu
Ahmad mai lamba ta: 25681
Don neman karin bayani duba: Tafsirin Ibnu-Kathir 1/607.
Allah ne mafi Sani.
Dr.Jamilu Zarewa
8/11/2015
54. ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA
CONDOM?
Tambaya: Salam. Malam Allah ya karama daukaka da imani.
Shin mutum
54
zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa
Condom?
Amsa:
To dan'uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa
ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai
haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara
da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai
haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın
wanka. Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan
ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai
jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za'a sadu
da mace mai haila ba ko da an sa Condum .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
28/11/2015

55. JINI YA BARKE MIN, SABODA AN YI MIN WANKIN CIKI


Tambaya :
Assalamu alaikum Dan Allah inada tambaya macen da tayi
bari aka mata wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata
yadai baiyana jinin ciwo ne Shin zata dunga wanka ne
lokacin da zatayi kowace sallah?
Ko kuwa tsarki kawai zatayi lokacin sallah?
Amsa :
To dan'uwa Za ta yi tsarki kuma ta yi alwala ya yın kowacce
sallah, saboda hukuncinsu daya da mai istihâlâ, kamar
yadda Annabi saw ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish a
hadisin Ibnu Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayin
kowacce sallah, lokacin da ya tabbatar tana yın jinin cuta.
Allah ne mafi sani.
Don neman karin bayani duba: Risala Fi Dima'u Addabi'iyya:
45.
55
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
28/11/2015

56. BABU KOME GA MATAR DA TA FANSHI KANTA


Tambaya:
Salam malam menene sharadin dawo da mata bayan tayi
khul'i dan Allah ataimaka?
Amsa:
To dan'uwa idan mace ta fanshi kanta daga wajan mijinta,
ba zai iya yi mata kome ba, Amma zai iya shiga cikin
manema in ta yarda da shi, sai a sake daura aure ya biya
sadaki
Allah ne mafi sani .
Dr. Jamilu Zarewa
30\11\2015

57. LOKACIN YAYE YARO A MUSULUNCI


Tambaya:
Aslm ya Shaikh: Allah yaqara wa Dakta lafia amin. Don Allah
mallam wane lokaci ne mafi inganchi da ya dace a yaye yaro
daga barin shan nono a shariance? Nagode Allah yasaka da
alkhairi amin.
Amsa:
To dan'uwa ina rokon Allah ya amsa addu'arka, Lokaci Mafi
çika na yaye yaro shi ne: idan ya kai shekaru biyu, kamar
yadda aya ta: 233 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan,
saidai ya halatta a yaye yaro kafin ya cika shekaru biyu,
mutukar ba zai cutu ba, kuma iyaye guda biyu sun cimma
daidaito akan hakan. Don neman karın bayani duba: Tafsirin
Qurdubi 3/162. Allah ne mafi Sani.

56
Dr. Jamilu Zarewa
2/12/2015

58. A KWAI GADO GA MATAR DA MIJINTA YA MUTU


BATA GAMA IDDA BA?
TAMBAYA:
Assalamu alaikum Mal. mutum ne ya saki matarsa Bai dawo
da ita ba kuma bata gama idda ba sai ya rasu, shin zata ci
gadonsa?. Allah ya kara ma mal imani da ilimi mai amfani
Ameen.
AMSA:Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa
barakaatuhu, To dan'uwa
Idan miji ya saki matarsa , kuma ya mutu kafin ta gama idda,
to za ta ci gadonsa Mutukar saki daya ne ko biyu, saboda har
a lokaçın tana nan a matarsa, amma in uku ne babu gado a
tsakaninsu, haka nan idan fansar kanta ta yi, saboda ta
nisanta daga gare shi. Allah ne mafi Sani.
Dr Jamilu Zarewa
10/12 /2015

59. ZAN IYA SHAN MAGANIN TSAYAR DA HAILA


SABODA AIKIN HAJJI?
Tambaya: Garemu kamar haka? Shin ya halatta mace ta
tsayar da jinin haila saboda aikin hajji?
Amsa:
To 'yar'uwa ya halatta, mutukar likita ya tabbatar miki ba zai
cutar da ke ba, saidai tsayawa a Dabi'ar da Allah ya halicce
ki akai shi ya fi kyau, saboda shan magunguna irin
wadannan yana birkita kwanakin al'ada, kamar yadda
bincike ya tabbatar Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
57
21\12\2015

60. RABON GADON MATA-MAZA!


Tambaya:
Slm, idan mutum ya mutu ya bar mata-maza da 'yan'uwa,
yaya rabon gadon zai kasance?
Amsa:
To dan'uwa mata- maza shi ne wanda yake da al'aurar mace
da ta namiji, kuma ya kasu kashi biyu :
1. Akwai mara rikitarwa, wato wanda aka gane inda ya fi
karfi, kamar ya zama yana haila, kaga za'a riskar da shi da
mace wajan rabon gado, ko ya zama yana fitsari ta al'aurar
namiji, to wannan hukuncinsa hukuncin namiji a wajan rabon
gado, haka nan idan ya zama yana da gemu da gashin baki.
2. Mai rikitarwa, wannan shi ne wanda aka kasa gane inda ya
fi karfi, kamar ya zama yana fitsari ta ala'aura biyu, kuma ba
wanda yafi fitowa da karfi ko da yawa a cikinsu, ko kuma ya
zama yana da gemu, kuma yana haila. Idan har mata maza
ya balaga ba'a gane inda yafi karfi ba, to za'a ba shi rabin
gadon mace ne, da rabin gadon namiji. Duba : Attahkikat
almardhiyya fi-mabahithil-fardhiyya shafi na 206. Allah ne
mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
9/5/2015

61. TA YI BAKANCE, AMMA TA KASA CIKAWA, YAYA


ZA TA YI?
Tambaya:

58
Malam wata mace ce ta yi bakance za ta yi azumin Annabi
Dawud, wato yau ta yi azumi gobe ta sha, amma kuma yanzu
ta yi aure ta kasa, ya ya kamata ta yi ? shin akwai mafita ?
Amsa :
To dan'uwa Bakance makaruhi ne, haramun ne a wajan wasu
malaman, saboda Annabi s.aw yana cewa : "Bakance ba ya
zuwa da alkairi" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai
lamba ta : 1639. Saidai ya wajaba a cika bakance idan aka yi.
Wasu daga cikin malaman hadisi sun ta fi akan cewa idan
mutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai iya yin kaffarar
rantsuwa, saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim a
lamba ta: 1645 a sahihinsa, wanda Annabi s.a.w. yake cewa :
"Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce" . Duba Alminhaaj
na Nawawy 4/269
A bisa abin da ya gabata za ki iya yin kaffarar rantsuwa wato:
ciyar da miskinai goma, ko tufatar da su, ko kuma 'yanta
kuyanga, idan babu hali, sai ayi azumi uku, kamar yadda ya
zo a suratul Ma'idah aya ta : 89 .
Allah ne ma fi sani
Dr. Jamilu Zarewa
12\7\2015
62. WANDA YAKE GIDA, ZAI IYA HADA SALLOLI
SABODA RUWAN SAMA ?
Tambaya:
Assalamu alaikum. Allah karawa malam ilimi da fahimta.
Shin da Allah malam ko mutum zai iya hada sallah shi kadai
idan ana ruwa bashi da ikon zuwa masallaci? Nagode malam
Amsa:

59
To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar
zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada salloli saboda
ruwan sama, tun da ruhusa ce Allah ya bawa mutane, don
haka ta shafi kowa da kowa, wannan ita ce maganar
Hanabila kamar yadda Mardawy ya ambata a INSAAF 2\340.
2. Bai halatta ga wanda bai je sallar jam'i ba ya hada salloli
saboda ruwan sama, saboda an yi sauki ne ga wadanda za
su je masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa, wannan
wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah a gida, don
haka rahusar ba za ta same shi ba, sannan kuma shari'a ta yi
nufin ta kiyaye sallar jam'i shi ya sa ta saukaka wajan hada
salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse sallar jam'i ta
tozarta, wannan ita ce maganar Imamu shafi'i a littafinsa
Al'umm 1\195 A fahimtata maganar karshe ta fi inganci, don
haka wanda yake gida ba zai hada salloli ba. Allah ne mafi
sani
Dr. Jamilu Zarewa
9/11/2015

63. ZAN IYA AURAN DAN WASAN KWALLON KAFA?


Tambaya:Malam ina tambaya ne akan kwallon qafa, a kwai
wanda yake
Neman aurena sana'arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake
komai, malam ina kokonto akan wannar sana'ar tasa, kada
ya kasance sai anyi auren inji cewa ba halal bane, tunda ana
biyansa idan sukayi wasa, to shine malam ko
a taqaice a sanar dani wani abu akai, saboda musan
makamar mu, nagode•
60
Amsa:
To 'yar'uwa ına rokon Allah ya baki miji nagari, malamai suna
kasa kwallo gıda uku :
1. Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu
su hadu, su yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan
kam ta hallata mutukar ba ta kautar daga ambaton
Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga .
2. Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su hada
kudi su sayı kofi wanda a karshe kungiya daya za ta
dauka, wannan kam bai halatta ba, saboda daidai yake
da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a
tsakanin 'yan kwallo.
3. Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma
malamai sun ce haramun ne saboda asali musabaka da
wasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari'a
ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin
abin da aka togace, sannan akwai barna mai yawa a
cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan Kwallon
wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi da
kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan
har da doke-doke tsakanin kungiyoyin guda biyu. Idan
ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na na biyu ko
na uku, to ya wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki
ji, to auransa akwai hadari saboda zai ciyar dake da
haramun. Don neman karin bayani duba Fataawaa Al-
lajna Adda'imah 3/238 da kuma Fataawaa Muhammad
bn Ibrahim 8/116. Allah ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Zarewa
12/11/2015

61
64. INA YAWAN WAYA DA BURDURWATA, KO YA
HALATTA A SHARI'ANCE?
Tambaya: Dan Allah ina tambaya, Namiji ne yakeso ya qara
aure to shine bayan ya dawo gida da dare sai budurwar ta
riqa kiran shi ko kuma ta riqa turo txt, shikuma idan matarshi
tana kusa sai ya riqa avoiding amma da ta dan daga sai
shima ya fara responding ko ya kira ta, kuma idan asuba tayi
sai ta kirashi. To shine matar ba taso, dan Allah a Shari'ance
yana da laifi ko ba shi da? sannan matar zata iya neman ya
dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari'ance?
Amsa:
To dan'uwa yana da kyau ka san cewa matar da kake nema
aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka dinga
hira da ita ba, sai gwargwadon bukata.
Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana daga
cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya
kirga jin dadin zancen wacce ba muharrama ba daga cikin
ayyukan da Allah ya hana.
Duk wanda yake yawan hira da matar da ba muharramarsa
ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin
dadin zancen matarsa ta halal.
Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon
bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku, ku aikata
katon sabo, yana daga cikin ka'idojin shari'a toshe duk
hanyar da take kaiwa zuwa barna. Zunubi shi ne abin da ya
sosu a ranka kuma ka ji tsoron kar mutane su yi tsinkayo,
kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba
ta: 2553.

62
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
4/1/2016.

65. ZAN IYA HUDA HANCI SABODA KWALLIYA GA


MIJINA?
Tambaya:
Assalamu'alaikum, Malam dan Allah wata ce mijin ta yace
hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata
babu kyau a musulunci. Shin malam ya abun yake? Haramun
ne,ko kuwa tana iya hudawa tasa dankunne tayi kwalliya da
shi?
Amsa: Wa alaikum assalam, An tambayi sheikh Ibnu
Uthaimin akan Wannan mas'alar ta huda Hancı sai yake
cewa: Huda Hanci zai iya zama canza halittar Allah, amma
idan Garin da matar da ta huda hancin take ana yın ado a
hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi ayi
hakan. Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137. Haka
nan an tambayi Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad akan haka a
darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi
akan haka.
Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda
hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al'adarsu ce,
saboda ya tabbata sahaban Annabi s.a.w mata suna huda
kunnansu suna sanya 'yan kunnaye Kamar yadda hadisin
Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
4/1/2016

63
66. ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA
BATUN GADO DA TAKABA?
Tambaya:
Assalam pls. an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba
sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa, tambayata
anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi ?
Amsa: To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure
kafin ya tare da amaryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa
takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi
S.a.w. ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin
da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145,
wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
5\1\2016
67. NA YI WANKAN JANABA, SAI MANIYYI YA SAKE
ZUBO MINI ?
Tambaya:
Assalamu Alaikum tambayata itace idan mata ta sadu da
mijinta tayi wanka immidietly bayan ta gama tana zaune sai
taji sperm ya zubo mata shin zata kara yin wani wanka ko
kuma wanda tayi ya isa ?
Amsa:
Wa alaikum assalam, To idan sabuwar Sha'awa ce ta zo
mata, ta zubar da maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma
idan saboda saduwar da suka yi ne a baya : za ta wanke
wurin ne, ta sake alwala, amma babu bukatar sake wanka,
wanda ta yi na farko ya isa. Duba Bidayatu Almujtahid 1\48
da Insaf 1/232. Allah ne mafi sani

64
Dr. Jamilu Zarewa
2/1/2016

68. RASHIN ADALCI TSAKANIN 'YA'YA YANA JAWO


FITINTINU
Tambaya:
As-salaamu alaykum Malam Allah ya kara maka imani da
fahimta tambayata itace Mahaifinane yake nuna banbanci a
tsakanin mu sannan yana yawan zagin mahaifiyata
musamman in 'kanne na sunyi masa laifi sai ya kama zaginta
Sai na nuna masa rashin jindadina da wannan Al'amari har
ya kai ga mun daga ma juna murya. Karshe sai ya fara yimin
Allah ya isa yana tsine mun.
Amsa:
Ya wajaba uba ya yi adalci a tsakanin 'ya'yansa, Annabi
S.a.w. yana cewa: "Ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin
'ya'ya yanku" Wannan ya sa lokacin da Sahabi Bashir ya yiwa
dansa kyauta, ya nemi Annabi s a w. ya yi shaida akan haka,
ya tambaye shi: shin Duka 'ya'yanka ka yi musu kyauta? sai
ya ce A'a, sai manzon Allah ya ce: Ba ka so su zama daidai
wajan yi maka biyayya? ba zan yi shaida akan zalunci ba".
Bukhari da Muslim sun rawaito wadannan riwayoyi. Yin
adalci a tsakanin iyalai yana inganta tarbiyya, yana sanyawa
su ji tausayin Uba bayan ya girma, yana kara musu hadin kai
da son juna. Ya wajaba mazaje su Sani cewa: zagin
matayansu ya sabawa ka'idojin sharia, kuma hanya ce ta
tabarbarewar tarbiyya, domin Yaran za su rabu biyu, wasu
suna bayan mahaifinsu, wasu kuma Babarsu za su ga ta yi
daidai. Ya wajaba a tausasa harshe lokacin da za'a yi

65
magana da mahaifi saboda Allah ya hana fadawa Uba kalma
mara kyau ko yaya take, kamar yadda ya zo a Suratul Isra'i.
Ba'a son ana yın muguwar addu'a ga iyalai saboda in aka
dace da lokacin amsar addu'a za ta zamar masa matsala
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
16/1/2016

69. ZANCEN BATSA TSAKANIN MASOYA!


Tambaya:
Wai shin menene hukuncin saurayi idan suna hira da
budurwarsa sai ya dinga yi mata hiran matar aure? yana ce
mata sha'awa tana damunsa, ita kuma budurwar ba
bazawara ba ce, dan Allah mai matsayin hiran a shari'a?
Allah ya kara muku Basira da ikilasi
Amsa:
Bai dace saurayi ya dinga zancen sha'awa ba ga matar da
bai aura ba, tunda Shari'a ta haramta yasashshen zance a
aya ta : 3 a Suratul Muminun, kuma hakan yana iya kaiwa
zuwa ga zina, idan aka samu macen da ba natsatstsiya ba,
ko kuma Shaidan ya ratsa, Yana daga cikin manyan ka'idojin
sharia toshe hanyar da take kaiwa zuwa barna. Allah ne mafi
sani.
Dr. Jamilu Zarewa
22/1/2016

70. YAWO BABU DAN-KWALI A TSAKAR GIDA?


Tambaya:

66
Assalamu alaikum,Allah gafarta malam shin zan iya yawo
acikin gida ba dan kwali?
Amsa:
Mace zata iya yawo babu Dan kwali idan tana tsakanin 'yan
uwanta mata musulmai saboda al'aurar mace ga 'yar uwarta
mace musulma tana kasancewa ne tsakanin gwuiwa zuwa
cibiya, mutukar akwai mazan da ba muharramai ba to bai
halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al'ura ce in
ban da fuska da tafukan hannu. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
24/1/2016

71. HUKUNCIN AUREN HANNU (Masturbation)


Tambaya:
Assalamu alaikum, Allah ya kara ma malam lapiya da imani,
malam dan Allah menene hukumci masturbation (Istimna'i) a
musulunci
Amsa:
Wa alaikum assalam. To 'yar'uwa Babu nassi ingantacce
bayyananne yankakke da yake haramta wasa da al'aura har
maniyyi ya fito, saidai wasu malaman sun haramta auran
hannu saboda aya ta 6 a Suratul Muminun ta iyakance biyan
bukatar sha'awa ta hanyar matar aure ko bayi kawai,
wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan
bukata ta hanyar su.
Yin wasa da al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa
matsaloli a likitance, saidai yana daga cikin ka'idojin shari'a;
idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda za'a yi

67
sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata,
wannan yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta
auran hannu ga wanda ya ji tsoron zina kuma ba shi da halin
da zai yi aure.
Idan mu ka ce auran hannu haramun ne, saidai barnar dake
cikin zina tafi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki,
sannan tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi
'ya'ya gantalallu, marasa asali, wannan ya sa magana ta
biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu sharudan da suka
gabata. Don neman Karin bayani duba: Muhallah 12\407 da
Majmu'ul fataawaa 34/146. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
23\1\2016

72. AL'ADATA TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN


TSARA IYALI ?
Tambaya:
Assalamu Alaikum Malam don Allah ina da tambaya, don
Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyarawa akan
lokaci. Malam matsala ta haihuwa gareni duk haihuwa ta sai
anyi min CS, sai likita ya bani shawarar tsarin iyali don in
huta, sai daga nan al'adata Tarikice sai yazo yau bazan sake
ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to
ni dai wanka na nakeyi na cigaba da ibadata to malam
ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan Ramadan yazo
min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai
nayi wanka na cigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai
dauke, don sai da yamin wajen kwana goma sannan ya

68
dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama wannan
kwanaki goman shima. To malam ya azumin tawa take.
Amsa:
To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki a cikin alqur'ani ya
rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka
mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya
wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai
dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo
miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a
lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah
da azumi ba. Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda
hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo
(zubar da maniyyi a wajen farji yayin saduwa) a lokacin da
Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi
mai lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali
suna birkita al'ada, wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba
likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka gane
maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa. Allah ne mafi
sa ni
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
22/1/2016

73. KARAWA AMARYA YAWAN KWANAKI, SABODA


HONEY MOON
Tambaya:
Meye hukuncin mutumin da yana da mata sai yayi amarya
sai yayi mata visa suka tafi wata kasa wata daya a matsayin

69
honey moon, to meye hukuncin daya matar, ya zalumceta
kenan?
Amsa:
To dan'uwa Anas RA ya rawaito cewa: "Yana daga cikin sunna
In mutum ya auri budurwa kuma yana da wata matar, ya yi
mata kwana bakwai, in kuma bazawara ce kwana uku"
kamar yadda ya zo a Sunanu Attirmizi a hadisi mai lamba ta:
1139, wannan sai ya nuna kari akan haka ya sabawa sunna.
Amma Idan Uwar gida ta bada izni ya halatta ayi kari akan
haka, tun da ya halatta mace ta sarayar da hakkinta na
kwana, kamar yadda Saudatu ta bawa Nana A'isha
kwananta, lokacin da girma ya zo mata, ta ga Annabi s.a.w.
bai damu da ita ba sosai, kamar yadda Bukhari ya rawaito a
hadisi mai lamba ta: 4914, wannan sai ya nuna halaccin
sarayar da hakkin kwana, da yiwuwar yiwa amarya kari idan
uwar gida ta yarda. Allah mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
31/1/2016.

74. ZAN IYA AURAN WACCE NA YI ZAMAN DADIRO DA


ITA?
Tambaya:
As salamu alaikum, Malamai ya halarta musulmi ya
musuluntar da matar da yayi zaman daduro da ita bayan
hakan ya aure ta, limanmin da ya goyi bayan hakan yayi
daide? Please is very important"
Amsa:
Wa alaikum as salam, ya halatta sabida babu alaka tsakanin
dadironsu da auransu bayan ta musulunta Mutukar sun tuba,
70
saboda musulunci yana rusa abin da ya gabace shi na
zunubi kamar yadda ya tabbata a hadisin Amru bn Al'ass.
Idan musulmi ya yi zina ya tuba, to Allah yana gafarta
dükkan zunuban da suke hakkinsa ne, kamar yadda aya
ta:53 a suratu Zumar ta tabbatar hakan Allah ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Zarewa
1/2/2016
.
75. JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI
WATA HUDU?
Tambaya:
Assalamu Alaikum Dr dan Allah inada tambaya akan matar
da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata
daga baya kuma sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu
yakan iya dawowa ko bayan wasu awowi shin ya hukuncin
sallar ta ? zata jinkirta sallah sai jinin ya dauke ko zata rika
yin wanka duk sanda ya dauke tayi ramakon sallolin baya ne.
Nagode
Amsa:
To 'yar'uwa mutukar cikin ya kai wata hudu kuma jinin da
yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to ya zama jinin biki,
kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to
mutukar ya zo da sifar jinin haila (baki ko karni) to zai zama
haila, tun da a zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila.
In ya fita daga wadannan biyun zai zama jinin cuta ta yadda
ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake fita, za ki
iya jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallolin da
aka yi su kina da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne

71
mai sauki, babu kunci da damuwa a cikinsa, kamar yadda
aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi bayanin haka.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
3\2\2016

76. ZA MU IYA AURAWA KANWARMU DAN SHI'A?


Tambaya :
Assalamu'alaikum..da fatan malam yana lafiya.. Malam wata
kanwarmu ce ta kamu da son dan shi'a dake ungurmu kuma
mun yi kokarin rabasu saboda wasu daga cikin munanan
dabi'ar su kamar zagin sahabbai, mutu'a, zagin matan
Annabi da dai sauransu. Amma abin dai ya gagara. Saidai ya
tabbatar mana da cewa shi tinda aka halicce shi bai taba
aikata wadannan laifukan ba. Sannan kuma bai yarda da
hakan azuciya ko a baki ba. Illah iyaka yasan yana bin
zakzaky ne akan yana kiran hadin kai ga musulmi. Shi iya
wannan ne ya amsa amma ya barranta ga duk wani
munmunar akidar shi'a.
A iya zaman da mukayi dai ba muga yana aikata wani
kaba'irar ba dan a masallacin mu yake sallah tin tashin mu
dashi. Shin malam ya halatta mu bashi. Ko kada mu bashi.
Amsa:
To dan'uwa tabbas a cikin addinin shi'a akwai manyan
abubuwa wadanda suke warware musulunci:
1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai, tare da
cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da su a ayoyi
da yawa a cikin alqur'ani, duk wanda ya ce mafi
yawancin sahabban Annabi s.a.w. sun kafirta tabbas ya

72
karyata Allah, wanda ya karyata Ubangiji hukuncinsa a
fili yake.
2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa: Alqur'anin
da yake hannunmu bai cika ba, tare da cewa: Allah ya
tabbatar: zai kiyaye shi, har abada.
3. Rafidha 'yan shia sun tafi akan cewa Nana A'isha
Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita
daga abin da munafukai suka zarge ta da shi a ayoyi
guda goma a suratun Nur.
Duk da cewa da yawa daga cikin 'yan shi'a suna kore
wadannan aqidu, saidai ayyukansu da littatatafansu da
maganganunssu, suna karyata korewarsu. Shugabansu
Zakzaky yace ba ya zagin sahabbai, kawai sai muka gan shi
a zaune a Husainiyyar Zariya yana la'antarsu, Haka Yakubu
Yahya na Katsina shi ma ya yi ikrarin haka, sai ga shi mun ji
shi yana siffanta Sahabbai da 'yan PDP, yana ci musu
mutunci da cewa sun yi juyin mulki. Ya wajaba ka sani yana
daga cikin manyan aqidun 'Yan shi'a TAKIYYA wato yin karya
ga wanda ba dan shi'a ba, kuma duk wanda bai iya wannan
ba, to bai cika dan shi'a ba a wajansu, domin ginshikin
addininsu ce, don haka kar ka dogara da maganarsa.
Annabi s.a.w. yana cewa : "Idan wanda kuka yarda da
addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa" kamar
yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1084, duk
wanda addininsa ya kunshi abin da ya gabata, bai halatta a
aura masa mace ba, tun da Allah bai yarda da hakan ba,
kuma addininsa ba yardajje ba ne, Allah ya ba ta miji nagari
wanda ba dan shi'a ba. Allah ne mafi Sani.

73
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
6/2/2016.

77. TAYI WASIYYA DA RABIN DUKIYARTA, SHIN TA


INGANTA?
Tambaya:
Assalamu alaikum dan Allah malam tambaya nake yi akan
wasiya, wata tsohowa ce ta rasu ta bar danta guda daya, sai
kuma wani wanda ta rika tun yana jinjiri har ya girma sai
tace: idan allah yayi mata rasuwa a raba gidanta biyu a
bashi rabi shima dan nata ya dauki rabin, hakan ko ya
halatta?
Amsa:
Wa alaikum assalam, mutukar ba ta da wani gidan sai wanda
ta yi wasiyya da rabinsa, To wasiyyar ba ta inganta ba,
saboda Annabi s.aw ya hana yın wasiyya da sama da daya
bisa ukun dukiya, Ta bar danta mawadaci, ya fi ta bar shi
yana maula a wajan mutane, kamar yadda hadisi ya
tabbatar, a riwayar bukhari mai lamba ta: 3721. Allah ne
mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
17\2\2016

78. TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE?


Tambaya:
Malam wata tayi cikin shege da wani mutum, saita nemi
wani daban ya rufa mata asiri ya aureta. Yanzu sunyi Auren,
yaya hukuncin auren a Shari'a?
Amsa:

74
Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure
kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai
albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa.
Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar
da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura
mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma
idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba
wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an
daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure
a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce
ne kuma rusasshe. Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam
Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i
kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi
istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma
suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura
mata aure, to auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya
ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta
haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya
shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud:1847.
Don neman karin bayani duba: AL-MUDAWWANNAH AL-
KUBRAH 2/173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79
A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren,
saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma
za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren
to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci

75
tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa,
kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata. Allah ne mafi
sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
27\2\2016

79. INA YIN HAILA DUK SATI, MENENE HUKUNCIN


ALLAH?
Tambaya:
Assalamu alaikum. Mal. tambaya nake, mace ce sati-sati
take ganin al'adarta, tun lokacin da tayi fama da rikecewar
al'ada, daga baya zubar jini har na kusan wata daya, ta je
asibiti sun yi bincike da hotona lokuta dabam dabam ba'a
gane komai ba, amma sun bata magani da allura domin
daukewar jinin. Tun daga lokacin da jinin ya dauke sai jinin
Al'ada ya rinka zomata sati-sati, Asibiti suka ce yanzu kam
sai dai ayi Addu'a. tambaya mal. Shin zata bar sallah duk
sati saboda ganin jinin ko mi cece shawara? Nagode
Amsa:
To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki, ya rataya hukuncin jinin
haila ne da samuwarsa a aya ta: 222 a suratul Bakara, don
haka mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni)
to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai
dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, ya zubo
miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a
lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah
da azumi ba. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
28/2/2016
76
80. BA TA HAILA SAI DUK SHEKARA, YAYA IDDARTA?
Tambaya:
Assalamu alaikum malam ina da tanbaya: mace aka saketa
saki 3 anma bata yi jinni ba sai bayan shekara 1 yaya iddarta
za ta zama kenan?
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi
shekara uku, kafin ta kammala, saboda Allah ya rataye iddar
matar da aka saka, kuma ba ta yanke kauna daga haila ba
da jini uku, kamar yadda aya ta : 228 a suratul Bakara ta
tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
4/3/2016

81. JININ BARI, BA YA HANA SALLAH?


Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa, Mal. Ciki ne Na wata
daya sai nake bleeding har ance nayi bedrest shine nace
yaya matsayin Sallah ta? Zanci gaba da yi ne ko zan barta
har se nayi wanka?
Amsa:
Malama ya wajaba ki yı sallah, saboda jinin da kike gani jinin
barı ne, Jinin barin cikin da bai kai Wata hudu ba, ba ya
daukar hukuncin jinin haihuwa, saboda ba'a busawa dan
tayin rai ba a lokacin, wannan ya sa ba zai hana sallah ba.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu zarewa
5/3/2016
82. ZAN IYA WANKAN JANABA, BA TARE DA ALWALA
BA?
77
Tambaya:
Assalamu alaikum. tambayata Anan shine: Menene
hukuncin yin wankan janaba ba tare da yin alwala ba?
Amsa:
Ya halatta ayı wankan janaba ba tare da alwala ba, kamar
yadda ya zo a hadisin Ummu-salama, Saboda Annabi S.A.W
ya siffanta mata wankan janaba da cewa: "Ya ishe ki, ki zuba
ruwa sau uku akan kı sannan ki zuba ruwa a duka jikinki, in
kika yi haka, kin tsarkaka" kamar yadda Abu-dawud ya
rawaito, kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta:
251. A cikin wannan hadisin babu alwala, wannan sai ya
nuna wankan ya yi da waccar sifar da kika tambaya. Saidai
sifar da ta zo da alwala a hadisin Nana A'isha ita ce mafi
cika, kamar yadda malamai suka bayyana. Allah ne mafi
sani.
Dr. Jamilu Zarewa
6/3/2016

83. MACE, ZA TA IYA YIN FITSARI A TSAYE?


Tambaya:
Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakaatuhu, Don
Allah malam mene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko
namiji a Musulunci?
Amsa:
Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da
Bukhari ya rawaito cewa: "Annabi S.a.w ya je jujin wasu
mutane sai ya yı fitsari a tsaye"kamar yadda Bukhari ya
rawaito a hadisi na 222. Tare da cewa duk hukuncin da ya zo

78
dağa Annabi s.a w. yana hada mace da namiji, in ba'a samu
abin da ya kebance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai
jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar
da Allah ya yı mata.
Yana daga cikin Ka'idojin sharia gabatar da wajibi akan abin
da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai
zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba
ta ingantuwa saida ita. Duk hadisan da suka zo cewa Annabi
ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana
A'isha wanda Hakim ya inganta, in da take cewa : "Duk
wanda ya ce muku Annabi s.a.w ya yi fitsari a tsaye kar ku
gaskata shi" kamar yadda Nasa'i ya rawaito a hadisi mai
lamba ta: 29.
Malamai suna cewa : za'a dau maganarta akan tana bada
labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu
wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da ba koyaushe
take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka'idoji a wajan
malaman Usulul-fiqhi : Duk wanda ya tabbatar da abu za'a
gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda
ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya
buya ga wanda ya kore. Don neman Karin bayani duba :
Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa'I 1\26.Allah ne mafi
sani.
Dr Jamilu Zarewa
8\3\2016

84. INA SON KARIN BAYANI A KAN SALLAR WALHA?


Tambaya:

79
Asalamu Alaikum malam ya aiki malam, don Allah ya ka'idar
sallar walaha take ? Allah ya saka da Alheri
Amsa:
To 'yar'uwa sallar walaha ba ta da wani adadin raka'o'i na
musamman, Za ki iya yın raka'a biyu ko hudu ko shida da
sallama uku, mafi yawan abin da aka rawaito daga Annabi
s.a.w. a sallar walaha shi ne raka'a takwas, kamar yadda ya
yi ranar bude Makka, Bukhari ya ambaci kissar a hadisi mai
lamba ta: 5806. Lokacin sallar walaha yana farawa daga
sanda rana ta fara zafi, kamar yadda hadisin Muslim mai
lamba ta: 748 ya tabbatar da hakan, har zuwa dab da
karkatar rana daga tsakiyar sama. Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
9\3\2016
85. BABU HADISI INGANTACCE AKAN YAWAN
KWANAKIN HAILA!
Tambaya:
Na karanta amsar da malam ya bada wadda ban fahimce
taba, Abisa T
tambayar da akayi mashi. Ta zuwan jini duk sati tare da
cewa taje asibiti Amman sunce saidai tayi hakuri in na
fahimci tambayar. Hukuncin matar da take da irin wannan
lalura shine : Zata bar salla a duk lokacin da jini yazo mata in
lokacin yin al'adattane ko da ya doge harfiye da kwanakin da
takeyi mutukar bewoce kwana(15) ba, Amman in ya woce
haka zatayi wanka tayi salla don haila ba ta wuce kwana(15).
Amsa:

80
Abin da abokina ya fada shi ne fatawar Malikiyya da
Shafi'iyya, saidai babu ko hadisi daya da ya tabbata akan
cewa : jinin haila ba ya wuce kwana sha biyar, duk hadisan
da suka zo akan haka ba su inganta ba, daga ciki akwai
hadisin da aka rawaito cewa: "An tambayi Annabi s.a.w
game da tawayar addinin mace, sai ya ce: "Daya daga
cikinsu zata zauna rabin rayuwarta ba ta sallah" Ibnul Jauzu
ya raunana shi a littafinsa Attahkik 1/263 haka Annawawy
shi ma ya ce: hadisin karya ne, kamar yadda ya zo a
AlMajmu''u 2\405, Ibnu Abdulhady shi ma ya raunana shi a
cikin Tankihu attahkiki1\414, Baihaki a cikin Ma'arifatu
assunan wal-athar,2/145 yana cewa: Na nemi hadisin da
sanadi a littattafan hadisi amma ban taba ganinsa ba, Haka
nan Hanafiyya sun tafi akan cewa: Jinin haila ba ya wuce
kwana goma, saidai duk hadisan da suka kafa hujja da su
babu ingantacce a ciki, Duba Al-ilal Al-mutanahiyah na Ibnu
Al-jauzy 2/382.
Zance mafi inganci shi ne haila ba ta da wasu kwanaki na
musamman, kamar yadda sheik Ibnu Uthaimin ya tabbatar
da haka a littafinsa na Dima'uddabi'iyya, tun da Allah da
manzonsa sun rataya hukunce-hukuncenta ne da
samuwarta, don haka duk inda aka samu jinin haila da
sifofinsa (baki, karni) hukuncinta yana tabbata, saidai idan
ya kasance mafi yawan rayuwa ko dukkanta, a lokacin ne zai
zama jinin cuta. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
11\3\2016

81
86. MIJINA YA MUTU, TUN KWANA (40), KO ME YA
KAMATA NA YI?
Tambaya:
Asalamu Alaikum malam tambayata maitakaba bayan tayi
kwana Arba’in, in tayi wanka zata iya goga shuwa a
hammatarta?
AMSA:
To Yar'uwa ina rokon Allah ya jikan mijinki, akwai hukunce-
hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:
1. Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba,
har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da
kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara
take nuni zuwa hakan.
2. Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji
ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta:
2304, ya yi bayanin hakan.
3. Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar
yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar
da hakan,
4. Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali
ba, kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya
bayyana hakan.
5. An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo
a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304.
6. Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko
da rana ne ko da dare.
7. Za ta iya yin Magana da mazan ba muharramanta ba,
idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya
murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana
hakan.
82
8. Babu wani launi na kaya na musamman da aka
shar'anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba
kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su.
9. Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi
ba.
10. Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har
ma za ta iya bude gashin kanta, idan duk
muharramanta ne.
11. Ya haramta ga mai takaba ta yi aure, har sai ta
kammala iddarta wata hudu da kwana goma, kamar
yadda aya ta: 235 a suratul Bakara take nuni zuwa
hakan. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
15/03/2016

87. INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA


BA LAFIYA ?
Tambaya:
Slm, Dr. macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi,
sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon
tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake?
Amsa:
To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma
bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin
manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun,
kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.
Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar
da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda
iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma
bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa
83
falalarsa. Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki
cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar
wannan sababin?
Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya
fita ne ta hanyar jin dadi. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
21/03/2016

88. MAI TAKABA, ZA TA IYA FITA AIKIN GWAMNATI


Tambaya:
Assalamualaikm mal inada tambaya mace ce mijnta ya
rasu koma ta kasance tana aikin gomnati shin zata iya fita a
lokacin da take takaba?
Amsa:
Wa alaikum as salam, a zahirin maganar malamai, mai
takaba ba za ta je aikin gwamnati ba, tun da bai halatta mai
takaba ta fita ba sai lokacin tsananin lalura, aikin gwamnati
ba ko yaushe zai zama lalura ba, tun za'a iya ba ta hutu, in
har ta nema, In tana da yadda za ta cı abinci ya wajaba ta
amshi hutu, ko da babu albashi, saboda bin sharia shi ne
zaman lafiya, duk wanda ya kiyaye Allah, to shi ma zai
kiyaye shi, duk wanda ya yi hakuri Allah hakurkurtar da shi.
Amma idan ta rasa yadda za ta yi ta cı abinci sai ta hanyar
aikinta, to ya halatta ta yi da rana kawai, saboda Annabi
S.a.w ya halattawa matan shahidai a zamaninsa, zama a
gidan daya dağa cikinsu domin hira da debe kewa da rana,
lokacin da suka takuru da zaman kadaici, duk da ya wajabta
musu komawa gidansu in dare ya yi, Kamar yadda Baihaki ya
rawaito, wannan sai ya nuna lalura tana halattawa mai

84
takaba fita da rana, kamar yadda Ibnu-khudaama ya ambata
a littafinsa na Mugni 8/130. Duk da cewa wasu malaman
Hadisin sun raunana hadisin Baihaki da ya gabata, saidai an
samu kwatankwacinsa daga maganar Abdullahi dan Mas' ud
da Abdullahi dan Umar Allah ya kara musu yarda, maganar
Sahabi hujja ce, in har ba'a samu wani sahabin ya saba maşa
ba, kamar yadda yake a ilimin Usulul-fiqh. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
22/3/2016
89. ZAN IYA KOMAWA WAJAN TSOHON MIJINA, IDAN
NA BIYU YA SAKE NI, KAFIN MU SADU?
Tambaya:
Assalamu Alaikum Malamina. Fatan Alkhairi a gareka, da
fatan ka wuni lafiya cikin koshin lafiya. Malam dan ALLAH ina
da tambaya kamar haka: (Mutum ne ya saki matarsa har
saki (3) a lokuta daban-daban, to, sai wani bawan ALLAH
yazo ya aure, bayan ya aureta sai wata matsala ta shiga
tsakaninsu kuma ya saketa amma kuma ko sau daya bai
taba sadu da ita ba, to, yanzu Malam ko wancen tsohon mijin
nata zai iya mayar da ita, tun da gashi tayi aure amma
saduwace kawai ba'a yi da ita ba??? ALLAH ya kara taimakon
ka Malam.
Amsa:
Wa alaikum assalam, ina har ba su sadu ba, to bai halatta ta
auri wani ba, saboda lokacin da matar Rifa'ata ta auri wani
bayan mijinta ya sake ta, ta so ta rabu da mijinta na biyun,
ta koma wajan na farkon, kafin su sadu, Annabi s.a.w. ya
hanata, inda ya ce mata : "Dole sai kin dandana dadinsa, shi

85
ma ya dandana dadinki, kamar yadda Bukhari ya rawaito a
hadisi mai lamba ta:5372, wannan sai ya nuna cewa aya ta :
230 a Suratul Bakara, ba aure kawai take nufi ba, tana nufin
aure hade da saduwa su ne suke halatta mace ga mijinta na
farko, saboda aikin Annabi s.a.w. da maganarsa su ne suke
fassara Alqur'ani. Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa.
27/3/2016

90. TA YAYA ZAN IYA GANE MUKTARIN SALLAH DA


LALURINTA?
Tambaya:
Assalamu alaika mal don Allah amin bayanin yadda ake gàne
yanayin muhktari da lalurin sallan Asuba da Maghrib?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Muktari da laluri, lokuta ne da Allah ya
rataya hukunce-hukuncen sallah akan şu, a na gane
muktarin sallar asuba idan alfijir na biyu ya keto, ana gane
lalurin sallar asuba idan gari ya yi fayau, ana gane muktarin
sallar azahar idan rana ta karkata daga tsakiyar sama, ana
gane lalurin sallar azahar idan inuwar mutum ta yi daidai da
tsawonsa, ana gane lokacin la'asar zababbe ya shiga idan
inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa, ana gane lalurinta
ya shiga idan inuwar mutum ta ninka tsawonsa, ana gane
muktarin sallar magriba, idan rana ta fadi, Muktarin sallar
Isha yana shiga idan ragowar Jan rana ya buya (shafaki)
Bayan dare ya raba lokaci ne na lalurin magriba da Isha.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa

86
4/04/2016

91. 'YAR KISHIYA ZA TA IYA GADONA ?


Tambaya :
Assalam Dr barka da asubah, da fatan kuna lafiya, Allah ya
taimaka. mace ce ta rasu ta bar 'ya'ya maza biyu da mace
daya, da kuma 'yar kishiyar ta, shin 'yar kishiyar tana da
kaso, a cikin gadon? Allah ya saka da alkhairi.
Amsa:
Wa alaikum assalam, 'yar kishiya ba ta çıkın magada, don
haka za'a bawa 'ya'yanta ne şu raba a tsakaninsu, duk namiji
ya dauki rabon mata biyu, Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
28/03/2016

92. MACE, ZA TA IYA YIN AURAN KASHEWUTA?

Tambaya:
Assalamu Alaikum malam menene hukuncin wadanda sukayi
auran kisan wuta suka maida aurensu,kuma menene
hukuncin auren nasu?
Amsa:
Wa alaikum as salam, Auran kisan wuta bai halatta ba.
Saboda Annabi (S.a.w) ya la'anci wanda ya yi da kuma
wanda aka yi saboda shi, kamar yadda Tirmizy ya rawaito
kuma ya inganta shi. Idan miji ya yi aure da niyyar halattawa
mijin baya, auran batacce ne, amma idan mace ce ta yı da
wannan niyyar, kuma mijin da ta aura bai sani ba, to auran
ya yi. Saboda ba dole ba ne mijin ya sake ta. Yana daga cikin

87
Ka'idojin sharia: ‫ من ل فرقة بيده ل أثر في نيتتته‬Duk wanda babu
saki a hannunsa, to niyyarsa ba ta da tasiri.
Allah ne mafi sani
Dr jamilu Zarewa.
29/3/2016

93. MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA


TURARE TA FITA UNGUWA ?
Tambaya:
Assalam malam muna san karin bayani akansa turare ga
mata sufita, wani malami yace wadda ba matar aure ba zata
iya sawa?
Amsa:
Wa alaikum assalam, To'yar'uwa ya haramta ga mace Baliga
ta sanya turare, ta fita unguwaa, saboda fadin Annabi SAW:
"Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to
ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito, A
wani hadisin kuma yana cewa: "Duk matar da ta sanya
turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu. Nassoshin da
suka gabata suna haramta sanya turare ga mace
balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin
matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna
gamewarsu ga dukkan mata wadanda sharia ta hau kansu,
tun da ba'a samu abin da ya kebance wasu nau'i ba, sannan
kuma an haramta sanya turaren ne : saboda yana kaiwa
zuwa tada sha'awar Maza, wannan kuma baya bambanta
tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba. Allah ne mafi sani.
Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji
kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada. haka ma budurwa, za

88
ta iya sanyawa a tsakanin 'yan'uwanta mata, ko gaban
muharramanta wadanda ta san ba za su yi sha'awarta ba.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
31/03/2016

94. IDAN NA KUSANCI MIJINA, YANA KYAMATATA,


MENENE MAFITA ?
Tambaya:
Assalamu alaikum MALAM nice ina da miji a duk lokacin da
zan zo kusa da shi sai yace min barci yake ji, ai sharia ta
hana na dameshi, a haka zamu yi kusan wata ba abin da ya
shiga tsakanina da shi, Allah taimaki MALAM menene mafita?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Ki tambaye shi dalılin da yasa yake yin
hakan, zai iya yiwuwa kin bata masa rai ko kuma akwai Wata
matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata
lamura za su iya fitowa fili. Sharia bata halattawa namiji yaki
saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau'ine na
cutarwa, yana dağa cikin manufofin aure katange ma'aurata
daga kallon haram.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
26/03/2016

95. MIJINA YANA SADUWA DA NI A RANAR GIRKIN


KISHIYATA ?
Tambaya:
Assalamu alaikum Mun kasance mu biyu awajen mijinmu,
Sai ya kasance yar'uwata bata iya gamsar dashi, to ko ranar
girkinta yakan shigo ya tara dani da rana ko da daddare,
tambaya anan shi ne malam shi hakan ya halasta? Kuma
89
idan na mishi magana ya daina zuwa baya ji, ba gidan mu
daya ba, Dan Allah hukuncin hakan da mafita?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Ya wajaba ya nemi izininta, tun da
hakkinta ne, in har ta sarayar ya halatta ya sadu da ke a
ranar kwananki da kwananta. Saboda lokacin da Nana
Saudah ta tsufa ta ji tsoron kada Annabi S.a.w. ya sake ta, ta
dauki kwananta ta bawa Nana A'isha, kamar yadda Bukhari
ya rawaito. Bayan haka Annabi S.a.w. yana yin kwana dai-dai
a dakunan matansa guda bakwai, ita kuma Nana Aisha yana
mata kwana biyu, Saudat kuwa ba ya kwana da ita, saboda
ta sarayar da hakkınta. Ya wajaba mai gida ya guji dukkan
abin da zai kawo matsala da fitintinu a tsakanin iyalansa,
adalci yana tabbatar da zaman lafiya. Allah ne mafi sani.
Dr jamilu zarewa.
15\4\2016

96. ANA BINA RAMAKON AZUMI, AMMA INA


KOKONTON YAWANSU ?
Tambaya:
Assalamu alaikum Mal. Mace ce ta sha Rabin azumi kuma
bayan azumin Ya wuce ta ranka Saidai ba duka ba yanzu
Tana so ta ida amma ta manta azumin Nawa tayi a baya
Tana ganin batayi rabi ba kuma tana ganin kamar tayi rabi
Amma ita ta manta DAN ALLAH MAL YA ZA TA YI??
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta yi gini ne akan tabbas wajan
ramako, misali idan kına zaton ashirin suka rage miki ko
kuma ashirin da biyar, to sai ki rama ashirin da biyar (25),

90
saboda in kin yi haka za ki fita daga kokwanto, kuma zai
zama tabbas kin rama abin da ake binki, ki rama abin da za
ki nutsu a zuciyarki kin rama. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
18/04/2016

97. INA SO NA SAN YADDA AKE ISTIBRA'I?


Tambaya: Assalamu ahlaikum Don girman Allah ina da
Tambaya ina so na
san yadda ake istibra'i da kuma dokokin su? Nagode
Amsa:
Wa alaikum assalam, ana yin istibra'i ne da jini daya a zance
mafi inganci, yana kasancewa ne ga matar da ta yi zina take
so ta tabbatar ciki bai shiga ba, kafin ta yi aure, kamar yadda
yake wajaba ga baiwar da mai gidanta ya sayar da ita bayan
ya take ta, kafin ubangidan ta na biyu ya fara saduwa da ita,
saboda kada a samu cakuduwar nasaba, matar da aka yi
mata fyade za ta yi istibra'i kafin ta yi aure. Allah ne mafi
sani
Dr Jamilu Zarewa.
20/04/2016

98. BA'A IDDAR SAKI DA WATA UKU!


Tambaya:
Assalamu Alaikum Malam ina da tambaya don Allah mace
ce tana shayarwa amma bata jini, sai mijinta ya sake ta, to
wai za ta kirga watannin ne na iddanta ko ya zata yi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Idan aka saki mace tana shayarwa, ya
wajaba ta jira tsarki uku, ko da kuwa za ta yi shekara uku

91
kafin ta gama, Ba'a idda da watanni uku sai ga wacce ba ta
fara haila ba, ko kuma wacce ta yanke kauna daga haila
saboda tsufa, kamar yadda aya ta: 4 a suratu Addalak ta
tabbatar da hakan. Allah ne mafi Sani.
Dr Jamilu Zarewa
22/04/2016

99. MIJINA ZAI IYA SIYAN KWANAN KISHIYATA, DON


YA KWANTA DA NI?
Tambaya:
Slm, ya halasta miji yasai kwanan kishiyanki ya biyata, don
ya kwana dake?
Amsa: Wa alaikum as salam, ban San dalilin da ya nuna ana
sayen kwana
ba, amma za'a iya nema mace ta sarayar da hakkinta na
kwanan,in har ta bayar ya bayu, tun da hakkinta ne, kamar
yadda Nana Sauda ta bawa Nana A'isha kwananta, saboda
tsananin son da ta ga Annabi s.a.w. yana Mata. Wannan yasa
Annabi s.a.w. yake kwana biyu a dakin Nana Aisha kamar
yadda ya tabbata a Bukhari, ragowar matansa bakwai kuma
yana musu kwana dai-dai, Nana Saudat kuwa ba ya kwana a
dakinta, bayan ta bawa Nana Aisha kwananta. Allah ne mafi
sani
Dr jamilu Zarewa
23/4/2016

100. DUK MINTI BIYU SAI NA YI TUSA, YAYA


SALLATA??
Tambaya:

92
Salamun'alaikum Malam Wai akwai sallah ga wanda in yana
sallah sai ya fitar da iskar tusa kuma duk sallah yake hakan
koda ace yayi kashi kafin yayi sallar, amma in har ya zo
sallah sai ta futo koda ace zayyi alwala sama da 10?
Amsa:
Wa alaikum assalam, akwai sallah akan shi, ba za ta taba
faduwa ba akansa, ya wajaba a gare shi ya yi alwala yayin
kowacce sallah, dağa nan duk abin da ya fito yana sallah ba
zai cutar da shi ba, tun da in aka ce ya sake alwala yayin
fitowar kowacce tusa ba zai iya ba, zai kuma shiga cikin
wahala, Sharia ba ta dorawa rai sai abin da za ta iya, kamar
yadda ayoyi da hadisai da yawa suka tabbatar da haka. Babu
takurawa da kunci a cikin Addinin musulunci kamar yadda
ayar karshe a suratul Hajji ta tabbatar da hakan. Don neman
Karin bayani duba: Alfawakihuddawany na Annafraawy
1\340.
Amma idan tusar ba'a mafi yawan lokuta take fitowa ba ya
wajaba ya sake alwala duk sanda ta fito, saboda sallah ba ta
ingantuwa saida alwala. Kula da wasuwasin abu ne mai
muhimmancin gaske, saboda da yawa Shaidan yake busa a
duburar dan'adam amma ba tusa ba ce, wanda ya ji haka, to
kar ya fita daga sallarsa, har sai ya ji iska ko kara ta fita,
kamar yada hadisin Bukhari ya tabbatar da hakan.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
24/04/2016

101. MACE ZATA IYA YANKE KITSONTA BAYAN


KAMMALA UMRA?
Tambaya:
93
Assalamu alaikum mlm inada tambaya don Allah in mutum
yayi umarah sai ya yanke gashinsa, amma na mace nake
nufi. Idan ta yi kitso zata iya kama jelar kitson daya ta yanke,
kuma kamar yaya za'a yanke gashin don Allah ina son
amsar dawuri Allah yataimaki mlm, yakara ma imani
Allahumma Ameeen.
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta iya kama gargawadon gabar dan
yatsa sai ta yanke daga dukkan kitsonta. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
28/04/2016

102. ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI?


Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Malam Barka da dare,
Malam ina tambaya ne dangane da wakilci a aikin hajji
(Anniyaabatu anil mayyit), mahaifina yana son yiwa wani
daga cikin makusantan shi da ya rasu; sai wani mutum
(malami) yake ce masa ai akwai addu'ar da ake yi (qul huwal
laahu sau wani adadi dss) wadda tafi wannan aikin hajjin da
za ai masa!! To dan Allah Malam yana so ne yaji shin hakan
ya tabbata, kuma dai-dai ne? ko akwai wani Malami da ya
fadi hakan?
Amsa: Wa alaikum assalam, Ba haka ba ne, wannan
maganar ba ta da asali,
Yiwa wani hajji ya tabbata a hadisai, wani mutum ya tambayi
Annabi (s.a.w) cewa: "Babana ya mutu bai yi hajj ba, zan iya
yi masa? sai Annabi (s.a.w) ya ce yaya kake gani Idan da

94
bashi ya bari za ka biya masa? sai yace E,sai Annabi (s.a.w)
yace to ai bashin Allah shi ya fi cancanta a biya, don haka ka
yi masa hajj, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya rawaito a
Muntaka hadisi mai lamba ta:1797, da kuma Darakudni.
Sannan Kathamiyya ta tambayi a Annabi (s.a.w) cewa: Hajji
ya riski babanta ya tsufa zata iyayi masa? sai Yace E, kamar
yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta;1756.
Malaman fiqhu sun kafa hujja da Wadannan hadisan
tabbatattu kan halacci ko wajabcin yiwa mamaci ko Wanda
bazai iya ba aikin hajji Idan yana da halı. Hajji ibada ce mai
zaman kanta,kuma daya daga cikin ginshikan musulunci
babu yadda za'a yi wata addu'a ta zauna a makwafinta.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
29\4\2016

103. ABUBUWAN DA ZA'A IYA FASA AURE SABODA


SU
Tambaya:
Assalamu alaikum, da fatan mallamai da dukkan 'yan uwa
sun tashi lafiya, Ina rokon Mallam bayani kan hukuncin
Wanda aka sanyama ranar aure kafin lokacin yace ya fasa.
Allah ya karama mallam lafiya da basira. Ameen
Amsa:
Wa alaikum assalam,in har akwai hujjar da sharia ta yadda
da ita, ba shi da laifi in ya fasa,kamar ya bayyana budurwar
ta sa ba ta da tarbiyya ko mazinaciya ce, ko kuma ba ta son
shi, ko tana da cutar da za ta hana a sadu da ita,kamar
toshewar farji ko hadewarsa da dubura, ko ya zama şu duka
suna da jinin da in sun hadu za su haifi sikila, yana iya fasa
95
auren idan ya zama ba shi da halin da zai iya ciyar da ita,ko
kuma likita ya tabbatar maşa ba shi da mazakutar da zai iya
saduwa da mace,haka ma idan ya ji ya tsaneta.
Dukkan abin da ake iya saki saboda shi, ana iya fasa aure ın
aka same shi, an shar'anta saki ne saboda tunkude cuta
daga ma'aurata ko daya daga cikinsu, yana daga cikin
ka'idojin sharia da kuma masu hankali: Tunkude cuta kafin ta
auku ya fi sauki fiye da kokarin kautar da ita bayan ta faru.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
3/5/2016

104. ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?


Tambaya:
Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace
Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?
Amsa:
Wa alaikumus salam, Bai hallata mutum ya rike hannun
wacce ba muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba.
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya
kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai
musu mubaya'a, yana yi musu mubaya'a ne da Magana,
kamar yadda ya tabbata a hadisi.
Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga Zina
saboda yana tayar da sha'awa, Allah Madaukaki ya haramta
kusantar zina a aya ta 32 a suratul Isra'i, Zina tana daga
cikin manyan zunuban da babu kamar su bayan shirka da
Allah. Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye

96
shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a
madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
05/05/2016.

105. YAUSHE ZAN FARA SADUWA DA AMARYAR DA


NA AURETA TANA KARAMA?
Tambaya: Assalamu alaikum, Ina fatar Allah ya kara ma
malam Ikhlasi.
Ya halatta idan mutum ya auri mace karama wadda bata fara
jini ba ya sadu da ita? Kokuwa rainonta zaiyi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Malamai sun cimma daidaito game da
halaccin aurar 'yar karamar yarinya, saboda aya ta hudu a
suratu Addalak ta bada labarin yadda karamar yarınya za ta
yi idda, hakan sai ya nuna ingancin yi mata aure kafin ta
balaga, sannan Annabi (s.a.w) ya auri nana Aisha tana 'yar
shekara shida.
Malamai sun yi sabani game da lokacin da za'a fara saduwa
da ita, bayan an yi auren,akwai wadanda suka tafi akan
cewa dole sai ta balaga za'a mikata ga mijinta. Wasu
malaman sun kayyade shi da shekara (9) saboda Annabi
(s.a.w) ya tare da nana A'isha ne bayan ta kai shekaru tara.
Zancen da ya fi zama daidai shi ne: za'a duba yanayin jikin
yarinyar, in har za'a iya jima'i da ita ba ta cutu ba,za'a iya
mikata ga mijinta, ko da shekarunta kadan ne, saboda mata
suna bambanta wajan girman jiki gwargwadon wurin da suke
rayuwa, da kuma irin abincin da suke ci, sannan sharia ba ta

97
iyakance lokacin da ake fara jima'i da mace ba. Don neman
karin bayani duba: AlMugni 27/77 da kuma Alminhaj na
Nawawy 9/206.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa.
09\5\2016

106. TA YI AURE RANAR DA TA GAMA TAKABA?


Tambaya:
Assalamualaikum malam meye matsayin auren da aka daura
randa mace tagama takaba ?
Amsa:-
Wa alaikum assalam, in har kwanakin iddar sun cika auran
ya yi, saidai Allah ya haramta neman aure cikin idda, in har
ya zama an fara neman auran ne tun kafin ta kammala
takaba, to tabbas an sabawa aya ta (235) a suratul Bakara,
saba dokar Allah yana jawo matsaloli. Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
16/05/2016

107. YA NEMI AURE A CIKIN IDDA?


Tambaya:
Assalamu Alaikum, Malam tambaya ne nakeso a taimaka a
amsa mun akan sha'anin aure. Malam mace ne tana zaune
da mijinta sae ya kasance zaman sun babu dadi, kullum a
cikin matsaloli iri-iri har ya kai ga takoma gidan iyayenta.
Iyayenta sun matsa mata se da ta tilasta mijinta ya saketa,
saboda suna da wani manufa akan idon ya saketa tsohon
saurayinta se ya aureta. Bayan ta matsawa mijinta akan lalle

98
ya saketa se mijin nata ya amince akan zai kawo mata
takardan sakin. Mallam a ranan da sukayi zai kawo mata
takardan sakin, kawai sae ta samu tsohon saurayinta akan ta
naso da zaran ta gama idda se ya aureta. Mallam menene
hukuncin wannan auren idon tagama idda ya aureta?
Na taba ji ance duk wanda ya nemi mace tana idda babu
aure a tsakanin su har abada, Mallam don Allah ka taimaka
mana da Karin bayani ?.
Amsa:
Wa alaikum assalam, in mutum ya nemi mace tana idda ya
aikata haramun, kamar yadda aya ta: (235) a suratul Bakara
ta tabbatar da hakan,saidai in an yi auran bayan ta gama
idda auran ya inganta, amma an aikata zunubin nema.
Malikiyya suna haramta mace ga mutum har abada in ya
aure ta cikin idda, ba in ya neme ta ba. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
19/5/2016.
108. ZAN IYA AURAN 'YAR KANWAR MATATA?
Tambaya:
Assalamu alaikum Malam, Ya halatta mutum ya auri yar
qanwar matarsa?
Amsa:
Wa alaikum assalam, ya halatta ya aure ta, bayan ya saki
matarsa, amma bai halatta ya hada su ba saboda innarta ce,
Annabi s.a.w. yana cewa: "Ba'a a hada mace da goggonta,
ba'a hada mace da innarta a auratayya, saboda in kuka yi
haka, za ku lallata zumunci ku" kamar yadda ibnu Hibban ya
rawaito.Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
99
20\5\2016

109. NA YIWA MIJINA KUL'I, KO AKWAI DAMAR


KOME?
Tambaya:
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, Dr muna
maka fatan alkhairi, tambayata ita ce auren da akai hul'i
yana halatta mijin ya maida matan, in kuma zai maidata,
shin zai sake biyan sadaki koko har abada ba suda aure?
Amsa:
Wa alaikum assalam, auran da mace ta fanshi kanta, daga
wajan mijinta yana halatta ta koma wajan shi bayan an sake
sabon aure da sadaki, ba sharadi ba ne sai ta auri wani kafin
a sake daura aure. Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
23/05/2016.

110. DAN ZINA ZAI GAJI MAHAIFIYARSA?


Tambaya:
Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam in nada
tanbaya, Malam mace ce tayi ciki ba tare da aure ba, ta
haihu kuma tana da kudi sai Allah ya mata rasuwa toh
malam yaron zai ci gadonta?
Amsa:
Wa alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta
haifi Da, daga baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta,
saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta :
10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, Dan zina kuma yana
cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.
100
Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi yawancin
malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.Don neman karin
bayani duba : Sunanu Attirmizy hadisi mai lamba ta: 2113 da
kuma Tabyinul haka'ik 6\214.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
25\5\2016

111. IDDA TANA FARAWA NE, BAYAN AN YI SAKI!


Tambaya:
Aslm alkm, malam Mace ce ta samu matsala da mijinta har
sukayi shekara daya bata gidansa sai daga baya yace ya
saketa, shin zatayi iddah ne ko kuma a'a?
Amsa:
Wa alaikum assalam, matar da aka saki bayan jimawa da
samun matsalar aure, iddarta za ta fara ne daga lokacin da
aka sake ta, Allah yana cewa a cikin suratul Bakara " Kuma
matan da aka saka za su zauna tsawon tsarki uku, kubutar
mahaifa ba ita ce manufar idda ba kawai, tunanin yiwuwar
daidaitawa yana daga cikin hikimomin idda, idan saki daya
ne ko biyu, kamar yadda aya ta farko a suratu Addalak ta yi
nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
27/5/2016

112. ZA KA IYA AURAN MACE BAYAN KA SAKI BABARTA!


Tambaya:
Malam mutun ne ya auri mace yana tsammanin budurwace
mai kananan shekaru, bayan sun tare sai ya gane cewa ba

101
karamar yarinya bace tana da shekaru masu yawa, Don haka
ba tare da sun yi saduwa na aure oay a saketa. Bayan haka
tafiya ta oay aoi zuwa wani gari inda acan yasami yarinya
mai irin shekarun da yakeso sai sukayi aure. Bayan auren sai
ya zaman wacce ya auran ‘ yar wancan mata oay a sakane.
To anan Auren ya halatta ko kuma bai halatta ba a bisa ayoyi
ko kuma Hadisai na Annabi (S.A.W)?
Amsa:
Wa alaikum assalam, idan mutum ya auri mace sai ya sake
ta kafin su sadu, ya halatta ya auri ‘yarta kamar yadda aya
ta: 23 a suratun Nisa’I da kuma hadisin da Tirmizi ya rawaito
suka tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa.
5/6/2016

113. INA SO NA SAN SIFFOFIN JININ HAILA?


Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don
Allah Tambaya gare ni Kan wani ruwa ke fitomin amma
kuma ba jini bane ina ganinsa kasa kasa babu wari ko qarni
tare dashi ina ganinsa idan nayi Azumi ko nayi aiki sosaise
marata tayi ciwo shine yake fitomin. Yaya Azumina da
sallahta take, shin zan cigaba da yinsu? sannan yana fitomin
wajan qarfe 3 na rana ne.
Amsa:
Wa alaikum assalam, mutukar ba jini bane, kuma ba baki ba
ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi
kyau ki je wajan likita don ya duba lafiyarki, saboda abin da

102
kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya
daga cikin siffofinsa. Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
7 Ramadan, 1437H (12/06/2016).

114. MACE ZA TA IYA YIN I'ITIKAFI?


Tambaya:
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh, malam
menene hukuncin ittikafin mata a musulunchi?
Amsa:
Wa alaikum asssalam, ya halatta mace ta yi i'itikafi, saboda
matayan Annabi s.a.w sun yi I'itikafi kamar yadda ya zo a
sahihil Bukhari. Yana daga cikin ka'idoji a usulul fiqhi duk
hukuncin da ya zo a sharia yana hade mata da maza, sai
idan an samu dalilin da ya kebance maza kawai. I'itikafi
ibada ce tabbatacciya a musulunci wacce Annabi s.a.w. ya
aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan
Ramdhana, babu banbanci tsakanin mace da namiji wajan
koyi da Annabi s.a.w a wannan ibadar, saidai kar matar aure
ta fita sai ta nemi iznin mijinta. Allah ne mafi sani.
Dr jamilu Zarewa

115. ZAN IYA BIYAYYA GA MIJINA WAJAN YIN


KULUMBOTO?
Tambaya:
Assalamu alaikum, Mallam mijina ne ya bani nama in dafa
masa amma ko wani yanka akwai alura a jiki sannan da
ruwan rubutu na dafa masa. Mallam naji tsoro kuma in banyi

103
ba zai kawo matsala tsakanin mu. Toh mallam yaya hukuncin
wannan abun?
AMSA: Wa alaikum assalam, ina ba ki shawara ki tambaye
shi, In har kin gano sihiri ne aka yi ya halatta ki ki dafawa, ko
da kuwa zai sake ki, saboda sihiri kafurci ne. Biyayya ga miji
dole ce kamar yadda hadisai da ayoyi suka tabbatar, saidai
babu biyayya ga abin halitta wajan sabawa mahalicci, kamar
yadda ayoyi a suratul Ankabuti da Lukman suka tabbatar da
hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa.
26 Ramadan, 1437H

116. YA YI BUDA BAKI DA JIMA'I DA MATARSA?


Tambaya:
Aslaam alaykum malam barka da warhaka da fatar kana
lapia. Malam
minene hukuncin Wanda yayi azumi amma bai yi buda baki
ba, ma'ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallah. Sai yayi
jima'i da matarsa, Ya azuminsa?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Azuminsa ya yi daidai, mutukar ya
sadu da ita ne bayan rana ta fadi. Annabi s.a.w ya yi umarni
ayi buda baki da dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali
kuma ayi da ruwa kamar yadda ya tabbata a hadisai, Yin
buda baki da dabino ko ruwa shi ne sunna, saidai wanda ya
fara da jima'i azuminsa ya inganta, tun da Allah ya halatta
masa jima'i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta:
187 a suratul Bakara ta nuna hakan.
104
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa.

117. ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA!


Tambaya:
Assalamu alaikum. Allah ya kara Ma Mallam Basira. Malam
Tambaya ta akan jinin haila ne. Malam an ce alaman da ake
gane karshen haila shi ne idan jinin ya canza kala zuwa
ruwan kasa. Na ga alaman hakan Se nayi wankan tsarki
Bayan haka Se kuma ya cigaba da zuba na kwana biyu
Malam tsarkin nawa yayi? Yaya matsayin sallah da azumi?
Nagode.
Amsa:
To 'yar'uwa abin da na sani daga malaman fiqhu shi ne: Ana
gane daukewar jinin haila ne ta hanyoyi guda biyu:
1- Kekasar kasanki ; Ta yadda mace za ta ga gabanta ya
bushe ko kuma tsumma ko always din da ta tare jinin
da shi.
2- Fitowar farin ruwa bayan daukar lokaci ana haila.
Idan jininki ya koma ruwan kasa kafin ki ga daya daga cikin
wadannan alamomi guda biyu, to ba ki gama haila ba, kuma
ba za ki dauki hukuncin masu tsarki ba, don haka azuminki
da sallarki ba su yi ba. Idan kika ga ruwa mai kama da kasa
bayan daukewar jinin haila, to ba zai cutar da tsarkin da kika
samu ba, kamar yadda hadisin Bukhari daga Ummu Addiya
ya tabbatar da hakan. Don neman karin bayani duba:
Addima'uddabi'iyya shafi na: 14.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu zarewa.

105
10/7/2016

118. YADDA AKE SADUWA DA MAI CIKI?


Tambaya:
Malam na kan ji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta
idan matar mutum tana da juna biyu ya yi jima'i da ita har
sai ta haihu meye gaskiyar maganar?
Amsa:
To dan'uwa ya halatta a sadu damace lokacin da take da ciki,
saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada
ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud : 1847
Ibnul kayim yana cewa :"Wannan hadisi yana nuna cewa ciki
yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi
da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta
ruwa" Tahzibussunan 1\193 .
Masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga hawa kan
matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho
yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda
kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron .
Sannan yawanci mata ba su cika son yawan saduwa ba idan
cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a
karanta saduwa a wadannan lokutan.
Allah ne ma fi sani .
Dr. Jamilu Zarewa
13-7-2017
106
119. MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI?
Tanbaya:
Assalamun alaykum Warahmatullahi wabarakatuhu bayan
sallama irin ta musulunci malam inayi maka fatan alheri
Allah yasa kana cikin koshin lafiya. Tanbayata malam ya
halatta mace ta yi alkalanci a musulunci, Allah yakarawa
malam lafiya.
Amsa:
Wa alaikum assalam, a wajan mafi yawan malamai mace bai
halatta ta yi alkalanci ba, saboda hadisin Abu-bakrata wanda
Annabi (s.aw) yake cewa: "Duk mutanen da suka jibintawa
mace lamuransu ba za su rabauta ba" kamar yanda Bukhari
ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4425.
Alkalanci yana bukatar nutsuwa da daidaiton yanayi, wannan
yasa Annabi (s.a.w) ya hana wanda yake cikin fushi ya yi
alkalanci, kamar yadda Muslum ya rawaito, mace kuma idan
ta fara jinin haila takan fita daga daidaito, ta yi abin da bai
dace ba, wannan yake nuna rashin dacewarta da wannan
aiki na Annabawa da manzanni.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
13/07/2016
120. MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE?

Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahamatullahi wabarakaatuhu: Miji ne
ya je saduwa da matar sa sai ya kuskure ya saka mata a
dubura shin mene ne hukuncinsa?
Amsa:

107
Wa alaikumus salam wa rahamatullahi wa barakaatuhu, In
har da kuskure ya saka mata a dubura, sai ya yi maza ya
zare, mutukar ya cire daga zarar ya ji ba wurin ba ne Allah
ba zai kama shi da laifin hakan ba.
A karshen suratul Bakara "Ya ubangijinmu karka ka kamamu
in mun manta ko munyi kuskure" Muslim ya rawaito hadisi
cewa: Allah ya zartarda hakan. Ibnu-majah ya rawaito hadisi,
Annabi s.a.w. yana cewa: "Allah ya yafewa al'umata abin da
suka aikata cikin kuskure". Cigaba da jin dadi a wurin bayan
gano kuskuren, yana daga cikin zunubai. Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
11 Shawwal, 1437 (16/07/2016).

121. MA'AURATA ZASU IYA KALLON TSIRAICIN


JUNANSU?

Tambaya:

Assalamu alaikum mallam menene matsayin kallon tsaraicin


ma’aurata?

Amsa:

Wa'alaykumussalam. Ya halatta ma'aurata su kalli tsaraicin


junansu, Saboda Annabi s.a.w. yana wankan janaba da
matansa, kamar yadda hadisai suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa
26/09 /2016

108
122. MEYASA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A
WAJAN RABON GADO?
Tambaya:
Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke
kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji
wajen rabon gado?
Amsa:
Wa'alaikum assalam, Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya
fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin haka,
saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar.
Allah da kansa ya raba gado bai wakilta wani don ya raba ba,
ya bawa kowa hakkinsa gwargwadon kusancinsa da mamaci
da kuma masalahar da Allah ya duba, wacce ya fi kowa
saninta.
Daga cikin hikimomin da suka sanya shariar Musulunci ta
bambanta tsakanin mace da namiji a rabon gado shi ne:
kasancewar hidimar namiji ta fi ta mace, yawanci mace idan
tana karama tana karkashin kulawar mahaifinta, idan kuma
ta yi aure tana komawa cikin kulawar mijinta.
Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya
sabawa ayoyin rabon gado a cikin suratun Nisa'i aya:14,
kamar yadda ya yi alkawarin Aljanna mai koramu ga wanda
ya bi rabon da ya yi a cikin aya ta:13 a waccar Surat. Duk
Wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai kiyaye shi, Wanda
ya sabawa Allah, to yana nan a madakata, kuma mabuwayi
ne mai tsananin karfi kamar yadda ayoyin Alqur'ani masu
yawa suka tabbatar. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa

109
05/10/2016

123. SHIN SUNAN RUMAISA'U YANA DA ASALI?


Tambaya:
Assalamu alaykum Malam menene asalin sunan Rumaisa ko
Rumassa'u kuma a zamanin Annabi akwai mai sunan in
akwai a bani tarihin ta?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Rumaisa'u suna ne na daya daga cikin
sahabbai mata, ita ce ta haifi Anas Dan Malik hadimin Annabi
(S.A.W) ita ce ta kai shi wajan Manzon Allah don ya dinga
masa hidima, ta auri Abu-Dalha, sahararren sahabi mutumin
Madina, an fi saninta da sunan Ummu-sulaim. Tana daga
cikin mataye masu hikima, akwai mahaddatan Alqu'ani da
yawa da suka fito daga tsatsonta. Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
11/10/2016

124. ZAN IYA AURAN WANDA YAKE DAUKE DA KWAYAR


SIKILA?
Tambaya: Assalamu Alaykum, don Allah ya halatta ya
hukuncin auran mace da genotype dinku daya da ita, AS AS,
ya halatta; sannan yana da fa'ida ko babu? Don Allah a
tambaya min malamai, na gode.

Amsa: Wa alaikum Assalam,Yana daga cikin ka'idojin sharia


tunkude cuta gwargwadon iko. Ilimin likitanci na zamani ya
tabbatar da cewa: idan AS da AS suka hadu za su iya haifar
Sikila (1) a cikin duk yara hudu ko biyar da za su Haifa.
A mafi yawan lokuta musamman a kasashen da talauci ya yi
musu katuutu, Sikila yana rayuwa ne cikin wahala, kuma

110
iyayansa ma a wahalce, Saboda raunin jininsu Wanda yake
haddasa musu ciwon wasu daga cikin gabobinsu.
Zai yi kyau ma'aurata su yi gwaji kafin aure, in har dukkansu
suna dauke da kwayar Sikila (AS) su hakura da yin aure tare,
tun da za su haifi yaron da zai rayu a wahale, da rashin
Walwala gashi kuma addinin musulunci ya yi nufin sauki da
jin dadi ga al'uma. Dukkan wani abu ba ya faruwa sai da
kaddara, saidai riko da sababi abu ne da sharia ta tabbatar,
kuma ayoyi da yawa suka yi bayaninsa. Wanda yake (AS)
idan ya auri (AA) za su haifi 'ya'ya lafiyayyu da iznin Allah,
wannan sai ya nuna abin yana da yalwa.
Allah ne mafi Sani
Dr. Jamilu Zarewa
12/10/2016

125. MIJINA YA SADU DA NI, KAFIN NA YI WANKAN


HAILA?
Tambaya:
Assalamu alaykum, Malam inada tambaya, malam mi ar
hukuncin mace taqare haila ba tayi wanka ba mijin ta ya
sadu da ita?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Maganar mafi yawan malamai shi ne:
ta jira sai ta yi wanka kafin su sadu, kamar yadda suka
fahimta a aya ta 222 suratul Bakara, amma Abu-hanifa yana
ganin halaccin haka, saboda ya fahimci tsarki a ayar da
yankewar jinin haila kawai. Riko da mazhabar farko shi ne ya
fi saboda Allah ya kira haila da kazanta. Babu wata kaffara
ga wanda ya sadu da matarsa kafin ta yi wanka bayan
yankewar jinin haila. Allah ne mafi sani:
Dr Jamilu Zarewa
111
2/11/2016

126. HAILA TA SAME NI BAYAN MIJINA YA SADU DA

NI.
Tambaya:
Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya,mace ce bayan
mijinta ya sadu da ita, kafin ta yi wanka Sai jini ya xo mata
ya xa ta yi wanka, shin gabadai zatayi niyya ko kuma
wannan na biyun xa tayi?
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta
yi wanka daya kawai. Yana daga cikin ka'idojin SHARIA Idan
ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda
daya, sannan za'a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta
shiga cikin dayar. Wannan yasa mai janabar da jinin haila ya
same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da wankan karshe,
saboda saukin musulunci da kuma daukewa jama'a abin da
zai kuntata musu, kamar yadda aya ta karshe a suratul Hajj
ta tabbatar. Allah ne mafi Sani
Dr Jamilu Zarewa
11/09/2016

127. TARON SUNA GA MATA HALAL NE?


Tambaya:
Assalamu Alaikum, Malam don Allah menene hukuncin taron
bikin suna a Musulunci ?
Amsa:
Wa alaikum assalam, A zahiri taron sunan da mata suke yi
al'ada ne, tun da mata ba sa yinsa da nufin samun lada ko
112
karawa abin da aka haifa albarka. Mata suna yinsa ne don
taya juna farin ciki, da kuma nuna annashuwa saboda
karuwar da aka samu, wannan yasa haramta shi yake
bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amalolin mutane a
bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wadda take
taron suna ba tare da ta riya cewa ibada ba ce hana ta ko
bidi'antar da taron yana da wuya, tunda bamu da dalilin
SHARIA daya haramta. Idan a cikin taron aka samu bidi'o'i ko
kuma ayyukan da Allah ya haramta kamar fito da tsaraici, ko
zancen da Allah ya hana, hakan zai iya zamar da shi
haramun, saboda yana daga cikin sharudan lura da al'ada
kar ta zama da sabawa nassoshin SHARIA, ko kuma ka'idojin
da malaman musulunci suka cimma daidaito akan su, kamar
yadda malaman Usul da na Kawa'idul Fiqhiyya suka ambata.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
7/11/2016

128. ZAN IYA AURAN WANDA IYAYANSA BA MUSULMI BA?


Tambaya:
Assalamu alaikum, Dr ya halatta mace ta auri wani wanda
Baban shi ba musulmi ba ne?, amma Mahaifiyar shi musulma
ce?
Amsa:
Wa alaikumus salam, Ya hallata mana ko da kuwa duka
iyayansa arna ne. Babban abin lura a wajan aure shi ne
addinin Wanda ya zo neman aure, saboda fadin Annabi,
sallallahu alaihi wa sallama: "Idan Wanda kuka yarda da
addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa". Tirmizi
113
ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084, kuma Albani ya
kyautata.
In kika lura za ki ga hadisin ya yi magana ne akan mutumin
ba iyayansa ba. Akwai sahabban Annabi, sallallahu alaihi wa
sallama, da yawa wadanda iyayensu ba musulmai ba ne,
amma wannan bai hana a aura musu 'ya'ya ba, irinsu
Sayyadina Aliyu dan Abu-Dalib da Abu-Ubaidah da saurasu.
Mahaifin sayyidina Aliyu Abu-dalib bai musulunta ba, Amma
kuma an aura masa shugaban Matan Aljanna Nana Fadima,
Allah ya kara yarda ga mata da mijin. Allah ne mafi Sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
12/11/2016
129. KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA!
Tambaya:
Assalamu alaikum Mal dan Allah ga tambaya nan Nice nai
aure na rabu da mijina, wato ya bani takardan saki, kafin ya
bani wannan takardar,mun samu matsala na bar gidanshi
tsawon shekara daya da wata tara,kuma Daman tsawon
zaman mu tare shekara bakwai ban taba samun ciki ba, yaya
iddata zata kasance?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za ki jira tsarki uku, tun da kun taba
kwanciyar aure kamar yadda aya ta 228 a Suratul Bakara ta
tabbatar da hakan.
Hukunce-hukuncen Saki suna farawa ne daga lokacin da aka
yi saki, ba daga sanda aka samu hatsaniya ba. Allah ya
shar'anta idda saboda manufofi da yawa daga ciki akwai:
bawa miji damar kome Idan saki daya ne ko biyu, ta yiwu
wani daga cikin ma'aurata ya yi nadama, Tare da cewa
114
babban makasudin shi ne tabbatar da kubutar mahaifa,
Amma ba shi kadai ba ne.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
25/11/2016

130. HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA


Tambaya:
Assalamu Alaikum! Mallam ina tambaya idan mutum ya
sadu da matarsa tana haila me ya kamata yayi? kuma ina
neman cikekken bayani mallam.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Wanda ya sadu da matarsa tana haila,
ya wajaba ya yi istigfari saboda ya aikata abin da Allah ya
hana a aya ta: 222 a suratul Bakara, Wannan ita ce maganar
mafi yawan malamai kamar yadda Ibnu Rushd ya fada a
Bidayatul mujtahid. Hadisin da ya zo na cewa: (Wanda ya
sadu da matarsa tana haila ya yi sadaka da rabin dinare) bai
inganta ba, wannan yasa ba za'a iya gina hukunci akansa ba.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
27/11/2016
131. MAGANIN ZAFIN NAKUDA?
Tambaya:
Assalamu alaikum, Don Allah Malam a taimaka mana da
addu'ar nakuda Don muna hanya ko yau ko gobe Allahu a
'alam. Allah yasa kawa Malam da gidan aljannatul firdausi.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Ban san wata addu'a ta musamman ba
wacce Mai nakuda za ta karanta, amma za ta iya karanta
addu'o'in da suka tabbata a Sharia ana karantawa saboda
tunkude tsanani kamar:
115
1- ‫اللهم ل سهل إل ما جعلته سهل وأنت‬
‫تجعل الحزن إذا شئت سهل‬.
2. ‫ل إله إل أنت سبحانك إني كنت من‬
‫الظالمين‬.
3. ‫حسبنا الله ونعم الوكيل‬.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
4/12/2016.

132. YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KO ZASU IYA AURE?

Tambaya: Assalamu alaykum. tambaya malam saurayi da


budurwane shaidan ya shiga tsakaninsu har ya kai ga
saurayin ya tsotsi qirjin budirwan har saida ruwa ya fito.
Hakan yafaru ba so dayaba ba biyu ba amma bata taba
ganin ruwanba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu,
ya halatta suyi auren? Kuma minene hukuncin shan Ruwan
da yayi
Amsa:
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa wannan abin da suka aikata
mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taba jikin matar da
ba ka aura ba, kuma kofa ce da za ta kai zuwa zina, idan
mutum ya tsotsi nonan mace bayan ya girma Amma babu
ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu aure ba, amma
idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan hakan
zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta su angunce, saboda kasancewar nonon da yake
haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika
shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da take

116
haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa” ,
Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya
wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma
wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi
tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi
yawan malamai.
2. Yana haramta aure, saboda ko da yaushe mutum ya sha
nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.a.w.
ya umarci matar Abu- huzaifa da ta shayar da Salim, don ta
haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi
mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya
girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono
to zai yi tasiri wajan haramcin aure.
Zancen da ya fi karfi shi ne nonon da mutum ya sha bayan
ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta ba
shi.
Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67.
Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai kiyaye shi,
Wanda ya saba masa zai same shi a madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
26/12/2016

133. INA DA SHEKARU (28), WACCE MACE YA KAMATA

NA AURA?
Tambaya: Assalamu alaikum, dafatan Malam yana cikin
qoshin lfy Allah sa haka amin. Malam inaneman shawara,
Wace mace yakamata na aura amatsayina na dan shekara

117
ashirin da takwas 28-29. yar shekara nawa tafi dacewa dani
a yanzu? Allah sa mudace amin .
Amsa:
Wa alaikum assalam, ka auri mai addini, wacce Idan ka
kalleta za ta burge ka, mai sonka, mai nutsuwa da sanin ya
kamata, yana da kyau ka Sami matar da ka fi ta kudi da ilimi,
ta fi sonka, ta kuma fika kananan shekaru, Ka tsaya ka
kalleta da kyau, kafın ka aure ta, kada ka yi gaggawa. Allah
ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
16/03/2016

134. MUNA JINKIRTA WANKAN JANABA ZUWA


BAYAN ASUBA, A WATAN RAMADANA?
Tambaya: Assalmu alaikum, malam ina da Tambaya shin
meye hukuncin matan da za su sadu da mijinsu lokacin
azumi, amma ba za su yi wanka ba har sai alfijir ya fito, shin
yaya matsayin azumin su yake? Nagode
Amsa: Wa alaikum assalam, ya halatta mace ta sadu da
mijinta su jinkirta wanka zuwa bayan ketowar alfijir a watan
Ramadhana, Azuminsu kuma ya inganta, saboda Annabi
(S.A.W) yakan yi haka da matansa, kamar yadda iyalansa
A'isha da Ummu Salama suka rawaito hakan, kuma Muslim
ya fitar da riwayar a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 1874.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
21/05/2016

118
135. MAI HAILA ZA TA IYA TABA IZU GOMA?
Tambaya:Assalamu Alaikum, Malam. Wai gaskia ne mace
mai haila (period) zata iya rike Alqur'ani izu gima?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Abin da yafi zama daidai Shi ne: kar
mai haila ta taba ko da wani bangare ne na Alqur’ani, saboda
hadisin Amru Bn Hazm, wanda wasu malaman hadisin suka
inganta, Inda Annabi S.a.w. Yake cewa: (Kar Wanda ya taba
Alqur'ani sai mai tsarki), kamar Albani a Sahihi wa dha'ifil
Jami'I hadisi mai lamba ta: 13738. Amma ya halatta ta
karanta ta hanyar kallo, saboda duk hadisan da suka hana
mai haila karatun Alqur'ani ba su inganta ba.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
4/01/2017

136. NA KASA BAMBANCE TSAKANIN JININ BARI DANA


HAIHUWA, YAYA ZAN YI?
Tambaya:
Assalamu alaikum. mallan nice nake yawan yin
bari( misscariage) sai wata ya kama nayi al'ada anma ba
kaman yanda na saba ganin jinin al'adar ba domin kuwa bai
zuwa da dan yawa kaman yanda nasaba ganin jinin al'ada
bai wuce naganshi dis dis ba a wano toh mallam bayan
kwana uku sai ya tsaya anma tundaga wan nan bansake
ganin jinin ba kuma nayi gwajin ciki wanda akeyi na fitsari
anma bai nunamin akwai ciki na bayan wani watan ya tsaya
saina fara ganin jini shima ba yanda na saba ganin jinin
al'ada ba sai ciwon ciki da mara qarni sosai gashi jajawur ga

119
wani dan kitse da wani zare zare da yake fitowa:shin dan
Allah mallam ya zanyi na banbance jinin bari dana haila
kasancewar nayi bari akai akai harsau 5 haihuwa 1.
Amsa:
Wa'alaykumussalam, Duk jinin da kika gani a BARIN da kika
yi bayan ciki ya kai wata hudu, sunansa jinin haihuwa, in
kuma bai kai ba sunansa jinin bari wanda baya hana sallah.
Dr Jamilu Zarewa
21/01/2017

137. SHIN WATANNI NAWA MIJI ZAI IYA KAURACEWA


MATARSA TA SUNNA?

Tambaya‫ ؛‬shin Tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya


kaurace wa matar shi ta sunna kuma wani Mataki ya dace ta
dauka in har ya wuce period din da sharia ta halatta?
Amsa:
Wa'alaykumussalam, Ya halatta ya kaurace mata tsawon
watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a suratul Bakara
aya ta: 226. Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da
kansa ya cigaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne
game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan
watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin
surar ta nuna hakan.
In ya ki komawa ya sadu da ita kuma ya ki saki sai taje wurin
Alkali don ya bashi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo
mata ko kuma ya sake.
Allah ne mafi Sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
10/02/2017

120
138. MIJINA YANA CHARTING DA TSOHUWAR BUDUWARSA,
BAYAN TA YI AURE
Tambaya:
Assalamu alaikum, Allah ya taimaki Dr, mijina ne suke chat
da wata matar aure, wadda tsohuwar budurwarsa ce a baya
sama da shekara 20 da wani abu ta yi aure, suna turawa
juna hotuna, shin malam wata shawara da nasiha ya kamata
na yi masa? Saboda kubutar da su ga fadawa halaka. Allah
ya taimaki mallam ya kara fahimta.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Ki yi masa nasiha da tsoran Allah,
sannan kuma ki nuna masa cewa: Inda matarsa ce ba zai so
ayi irin wannan mua'malar da ita ba. Yin charting irin
wannan da matar aure yana iya kaiwa zuwa zina,
musamman da alama har yanzu suna son juna, Allah ya
hana duk abin da zai kusantar zuwa Zina a suratul Isra'a'i.
Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi kuma ka ji tsoran kar
mutane su yi tsinkayo akai.
Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye Shi, wanda ya saba masa
zai hadu da Shi a madakata. Dayanku ba zai yi cikakken
imani ba har sai ya sowa dan'uwansa abin da yake soma
kansa. Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
4/4/2017

139. SHEKARA DAYA MIJINA BAI SADU DA NI BA,


MENENE SHAWARA
Tambaya:

121
Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah ya samu dace.
Malam don Allah ina son nasan matsayin aurena shekara
daya mijina be kusanceni ba alhalin muna tare kuma
dukkanin mu muna lafiya. Nagode .
Amsa:
Wa alaikum assalam, Auranku ingantacce ne,, amma zai yi
kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da
saduwar ma'aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure,
wanda rashinsa yana kai ma'aurata zuwa saɓon Allah. In har
ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya
kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai
Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4)
kamar yadda aya ta (226) a suratul
Bakara ta tabbatar da haka. Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
08/06/2017

140. INA SON CIKAKKEN BAYANI AKAN KUL'I?


Tambaya: Assalamu alaikum warahmatullah
wabarakatuhu. Malam ina so amin cikakken bayani akan
kul'I?
Amsa:Wa alaikum assalam, Khul'i shi ne mace ta fanshi
kanta daga wajan
mijinta ta hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta
kamar yadda matar Thabit Bn Kais bn Shammas ta yiwa
mijinta à hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan
musulunci. Ya halatta à shariar Allah mace ta yiwa miijnta
Kul'i in har ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokinsa na aure

122
ba, kamar yadda aya ta (229)a suratul BAKARA ta tabbatar
da hakan.
À zance mafi inganci Kul'i yana saukar da saki daya, saidai
yana nisanta mace da mijinta ta yadda ba zai iya saké zama
da matar ba, sai in ya bayar da SADAKI sannan an kara
daura sabon aure.Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
20/06/2017

141. WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU?


Tambaya:
Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji
ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa
ku?
Amsa:
Wa alaikum assalam, ta saku mana, saboda rubutu yana
daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. W. yana cewa
"Allah ya yiwa Al'uma rangwame akan abin da ta riya a
zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta aikata. Hadisin da ya
gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta
saku, saboda duk masu hankali sun cimma daidaiton cewa
rubutu aiki NE, shi kuma ya yi aiki. Yana daga cikin Ka'idojin
Shariar da malamai fada a littattafan fiqhu:‫الكتاب كالخطتتاب‬
Rubutu kamar magana NE.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
24/06/2017

123
142. TA HAIHU KAFIN TA CIKA WATA BAKWAI DA
AURE?
Tambaya: Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar
da ita ba tayi
wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara
(9) to malam
meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a
musulunci?
Amsa: Wa'alaikum salam,In har an San tana da ciki aka yi
auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai
inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi
Kafin ta cika wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to
dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi
sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.Auran dá
aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai
ba zá'à danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.
In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya
take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi s.a.w. "Duk
wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar
da ruwansa ga shukar waninsa" kamar yadda Abu-dawud ya
rawaito. In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta aure,
musamman in bai sani ba saí dá aka daura.Allah ne mafi
sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
07/08/2017

143. WANDA YA SAKI MATARSA A CIKIN MAYE, BA TA


SAKU BA

124
Tambaya:
Assalamu alaikum malam, tambaya ce dani. Mijina ne
yasake ni sau biyu, sai yasha abin maye yace na zo
nasameshi, nii kuma banzoba saboda bana son abin da
yakesha na maye, shine yace idan banzoba a bakin aure na.
Shin yaya auren mu? Allah ya saka da alheri.
Amsa:
Wa alaikumus salam, Malamai sun yi sabani game da
aukuwar sakin wanda yake cikin maye: akwai maganganu
guda biyu:
1. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan ya saki
matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon
Allah né, kuma shi ya jawowa kansa, don haka ba za'à
yi masa uzuri ba, wannan ita ce maganar Abu-hanifa da
Malik da Shafii a daya daga cikin zantukansu.
2. Sakinsa bai auku ba, saboda lokacin dá Má'iz ya zo ya
tabbatarwa Annabi S. A. W. ya yi zina saidá ya tambaye
shi ko ka sha giya né, kamar yadda Baihaki ya rawaito a
Sunanul-kubrah, hakan saí ya nuna mashayin giya ba'a
amsar maganarsa. Sannan an rawaito daga sayyadina
Usman da Ibnu Abbas cewa : sakin mashayin giya ba ya
aukuwa, kuma ba'a san wanda ya Sabá musu ba a cikin
Sahabbai.wannan ita ce maganar Imamu Ahmad da
Zahiriyya da Ibnu Taimiyya.
Babban Muftin Saudiyya na waccan lokacin Sheik
Abdulaziz bn Bazz da wasu Malaman suna rinjayar da
magana ta biyu saboda mashayin giya bai san abin da
yake fada ba, hakan sai ya sa ya yi kama da Mahaukaci
125
wanda Alkalami ya saraya daga kan shi, kai har sallah
ma an hana mashayin giya ya yi saboda ba ya cikin
hayyacinsa, kamar yadda aya ta (43) a Suratu Annisa'í
ta tabbatar da hakan. Don neman karin bayani duba :
Al-Mugni 7/289 dá kuma Sharhul Munti'i 10/233.
Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
9/08/2017

144. ZA MU IYA SANA'A DA WUTAR LANTARKI A


GIDAJAN GWAMNATI ?
Tambaya:
Assalamu alaikum malam, Tare da fatan Allah Ya karbi
ibadun mu da ku Alhazai baki daya. Malam ina hukunchin
wanda suke zaune a gidan hukuma, kudin wuta da ruwa duk
hukuma ke biya. Ya halatta suyi harkan kasuwanchi da ruwa
da wuta, kamar niqa gari, ko yin qanqara suna chin kudin da
suka samu. Ina matsayin wannan a Shari'a?
Amsa:
Wa alaikum assalam, In har a cikin albashinsa ake dauka
babu laifi in ya yi sana'a kamar yadda hakan yake faruwa a
cikin albashinmu na malaman jami'o'i, tun da hakkinsa ne
kuma in da ba ya shan wutar da ba'a cira a albashinsa.Misali
a A. B. U. Zaria hukuma tana cirar min dubunanai daga
Albashina duk wata, saboda wutar lantarkin GIDANA, kin ga
babu laifi in na yi Sana'a da wutar saboda na riga na biya.
Amma idan akwai sharadin da hukuma ta sanya na hana
amfani da wutar a wasu halaye da kuma lokuta ko wasu
kayan lantarki saboda kar asha ta wuce ka'ida ko gudun

126
fadawa hadari ya wajaba a kula da su, mutukar bai sabawa
sharia ba, tun da musulamai suna kan sharudansu ne kamar
yadda hadisi ya tabbatar.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28/08/2017

145. MAI TAKABA ZATA IYA FITA SALLAR IDI?


Tambaya:
Assalamu alaikum warahmatullah, Barka da war haka, Don
Allah ya halatta me takaba ta je sallar Eid?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Bai halatta ga mai takaba ba ta fita
zuwa Idi, saboda Hadisin Ibnu Majah Mai lamba ta: (2031)
inda Annabi SAW yake cewa da Furaia lokacin da mijinta ya
Rasu: (Ki zauna a cikin gidan da kika samu labarin mutuwar
mijinki har zuwa Ki kammala iddarki"
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Mai takaba ba za ta
fita ba sai in akwai lalura, sallar idi kuma ba ta cikin lalorori a
sharia. Imamu Ashshaukani a cikin Nailul Audaar 3/343 ya yi
bayani cewa "Dukkan Mata ana fitar da su daga gidanjansu
Don su halarci idi, in ban da wacce take iddar mutuwa".
Allah ne mafi Sani
Dr Jamilu Zarewa
03/09/2017
146. HUKUNCIN RATAYA LAYA DA GURU
Tambaya:
Assalam Alaikum.Malam, menene hukuncin amfani da LAYA
KO GURU a musulunci? Allah yasa mu dace.
Amsa:

127
Wa alaikum assalam,To dan'uwa Layu da guru sun kasu
kashi biyu:
1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko sunayan
aljanu ko wani abu na daban wanda ba Qur'ani ba,
wannnan malamai sun cimma daidaito game da
haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna
Adda'imah 1/212 saboda fadin Annabi S.A.W. (LAYU da
kuma abin da ake daurawa mace don miji ya sota shirka
ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai
lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da
hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta:
(16969), inda Annabi S.A.W. yake cewa: (Wanda ya rataya
laya to ya yi shirka), shima wannnan hadisin Albani ya
inganta shi a Silsila Sahiha. Hadisan da suka gabata suna
nuna haramcin daura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta
da shirka, shirka kuma tana fitar da mutum daga
musulunci.
2. LAYUN da aka yi su daga Alqur'ani ko hadisai ingantattu,
wadannan na'u'i malamai sun yi sabani akansu:
A. Sun halatta saboda sun kunshi sunan Allah da kuma
karatun alqur'ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da
su ya dogara ga Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-
ass da Aisha da wasu daga cikin magabata.
B. Ba su halatta ba saboda Ba'a samu Annabi S.A.W. ya yi
ba, da hakan sharia ne da an gan shi ya yi ko da sau daya ne
a rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da
Alqur'ani zai jawo a wulakanta su tun da za'a shiga wurare

128
marasa tsarki da su lokacin biyan bukata, kiyaye hakan
kuma yana da kamar wuya.
Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun da suke
daga Alqur'ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga
manzon Allah S.A.W, sannan shariar musulunci ta halatta
mana addu'o'i da yawa na neman kariya wadanda suka
wadatar da mu daga layu. Don neman karin bayani duba:
Taisirul Azizil Hamid shafi na : (136) da kuma Ma'arijul Kabul
2/510
Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
4/10/2017

147. SAURAYINA YANA LUWADI MENENE SHAWARA?


Tambaya:
Assalamu Alaikum Warahmatullah. Malam Barka Da Asuba.
malam wata 'yar'uwammuce take tambayata tana da saurayi
suna soyayya har an sa musu ranar aurensu amma yarinyar
sai ta gano saurayin aikinsa neman maza yan uwansa shine
take tambayata ta rufa masa asiri suyi aure ya halatta??.
Ahuta lafiya bissalam
Amsa:
Wa alaikum assalam, Ta sanya a yi masa nasiha ko ita ta yi
masa, in har ya tuba, tuba ingantacce za su iya yin aure,
saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba
aikatawa ba ne. In bai tuba ba ana iya fasa auran saboda
mai wannan aikin FASIKI ne, Annabi S.A.W. yana cewa: (Idan
wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku to
ku aura masa) kamar yadda Tirmizi ya rawaito. Mai neman
129
maza dabi'unsa ba yardaddu ba ne, wannan ya sa za'a iya
hana shi aure. Sannan bai kamata a rufa masa asiri ba,
musamman idan aka masa nasiha a asirce ya ki tuba saboda
Mabarnaci ne. In har za su yi aure ya kamata ayi gwajin jini
saboda yiwuwar ya kwashi wata lalurar ta hanyar masha'ar
da ya aikata a baya.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28/10/2017
148. MACE ZA TA IYA BAWA MIJINTA ZAKKA?
Tambaya:
Assalamu alaikum, Malam Menene sahihi kan mace tabawa
mijnta zakkah ?
Amsa: Wa alaikum assalam, ya halatta a zancen mafi yawan
malamai saboda hadisin Zainab matar Abdullahi Dan Mas'ud
wanda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta:(1462) da
kuma Muslim a hadisi mai lamba ta: (1000) lokacin da ta
nemi fatwa akan bawa mijinta sadaka kuma Annabi S A W. ya
halatta mata hakan. Malaman sun kafa hujja da wannan
hadisin saboda kalmar sadaka ta kunshi farilla da sunna. Aya
ta (60) a suratu Attaubah ta yi bayanin nau'o'i takwas na
mutanen da ake bawa zakka, daga ciki akwai talaka, hakan
sai ya nuna mutukar miji talaka ne matarsa za ta iya ba shi
zakka, tun da ba'a samu dalilin da ya fitar da shi ba. Saidai
Ibnul Munzir ya hakaito ijma'i cewa: "Bai halatta miji ya bawa
matarsa zakka ba idan tana fama da talauci, tun da zai iya
wadatata ta hanyar ciyarwar da Allah ya wajabta masa. Don
neman karin bayani duba: Sharhul Mumti'i (6/168) da kuma
Fataawa Allajnah Adda'imah (10/62) Allah ne mafi sani.
130
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/11 /2017

149. YA YI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN


YA YI KAFFARA?
Tambaya:
Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne ya yi
wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya
sake wani auren. Malam ya matsayin wannan sakin da
matsayin auren? Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga
Malam.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Auransa na biyun ya inganta saboda ba
su da alaka da juna.Wasu Malaman sun tafi akan cewa
mutukar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware, amma
in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai halatta ya taba ta
har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah
ya fada a cikin Al-Mugni.Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
01/06/2017.

150. AURAN KAFURAI KAFIN SU MUSULUNTA


INGANTACCE NE!
Tambaya:
Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min
malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya
musulunta shi da iyalan sa ta dalili na, kuma ni na basu
kalmar shahada. Suna da yara manya da kanana, sai suka
tambayeni ya ya matsayin auren su nace auren suna nan
kamar yadda shariar musuluncinta tsara, sai yace min to
yaya matsayin ‘ya’yan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba

131
shine nake son a mika min wannan tambaya ga malaman
Allah yataimaka amen.
Amsa:
Wa alaikum assalam, To ɗan'uwa auran da kafurai suka yi
kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan
ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu,
saboda Annabi S. A. W bai canza auran kafiran da suka
musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda
da 'ya'yansu da suka haifa ta hanyar wancan aure.
Sahabban Annabi S. A. W. da yawa an haife su ne ta hanyar
auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da
dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da
kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa
iyayansa bayan sun musulunta. In kafirai suka yi zina suka
haifi Ɗa ba za'a danganta shi zuwa babansa ba bayan ya
musulunta. Don neman karin bayani duba:
Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma
sharhulMumti'i12/239.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
13-09-1438/ 08-06-2017
151. TA KI YARDA DA MIJINTA SABODA TANA AZUMIN NAFILA!
Tambaya: AssalamuAlaikum.Mallam ina da tambaya? Yaya
hukuncin Matar da miji ya bukacheta tana Azumin sunna. Taki
ta aminche mishi
Amsa: Wa alaikumus salam, ta yi kuskure ya kamata ta amsa
kiran mijinta, saboda azumin sunna ya halatta a karya shi ko
da babu dalili, Annabi (SAW) yana cewa"Mai azumin nafila
sarkin kansa ne ina ya Ga dama ya cigaba da azumin, in

132
kuma ya so ya karya " kamar yadda Tirmizi ya rawaito a
Sunan.
Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
30/1/2018

152. MIJINA YA SAKE NI INA SHAYARWA, KO ZAN


IYA IDDA DA WATA UKU?
Tambaya:
Assalamu alaikum, Malam ga tambayata kamar haka watace
aka saketa tana shayarwa kuma ba ta yin al'ada to shin xa ta
iya yin aure bayan wata uku ko kuma sai tajira ta yaye
yaronta har taga al'adanta Kafin tayi auren nagode.
Amsa:
Wa alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi
shekara uku, kafin ta kammala iddar, saboda Allah ya rataye
iddar matar da aka saka, kuma ba ta yanke kauna daga haila
ba da jini uku, kamar yadda aya ta : 228 a suratul Bakara ta
tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
18/02/2018

153. MIJINA YA SAKE NI DA DANYAN GOYO, YAYA IDDATA


Tambaya: Assalamu Alaikum, Dr. macece mijinta ya saketa
bayan ta haihu da danyen goyo. Ya iddarta zata kasance?
Allah ya karawa Dr. Ikhlasi
Amsa: Wa alaikum assalam. Za ta jira jini uku Kamar yadda
aya ta (228) a Suratul Bakara ta tabbatar da hakan, ba za ta
yi aure ba har sai ta kammala su, Allah ya kara mana iklasi a
duka lamuranmu. Allah ne mafi sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
25/06/2018
133

You might also like